“Kina Son Dana?” Wata Uwa Ta Tunkari Kyakkyawar Budurwa da Ta Gani a Wajen Biki a Madadin Danta

“Kina Son Dana?” Wata Uwa Ta Tunkari Kyakkyawar Budurwa da Ta Gani a Wajen Biki a Madadin Danta

  • Wata uwa ta yi fice a soshiyal midiya saboda tambayar da ta yi wa wata kyakkyawar budurwa da ta hango a wajen wani biki
  • Kyakkyawar budurwar na taka rawa ne lokacin da matar ta tayata rausayawa sannan ta tambayeta ko tana son danta
  • Bidiyon ya haifar da martani mai ban dariya bayan an yada shi a TikTok inda matashiyar ta ce tambayar ta bata mamaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Mutane da dama sun yi martani kan bidiyon wata uwa da ta tunkari budurwa a madadin danta.

A wani bidiyo da ya samu mutum fiye da miliyan 6 da suka kalla a TikTok, an gano kyakkyawar budurwar na taka rawa kuma alamu sun nuna ta burge matar.

Kara karanta wannan

Maganar aure na rawa bayan saurayi ya sa budurwa ta girkawa danginsa su 70 abinci, gishiri ya zarce

Budurwa da wata mata suna taka rawa
“Kina Son Dana?” Wata Uwa Ta Tunkari Kyakkyawar Budurwa da Ta Gani a Wajen Biki a Madadin Danta Hoto: TikTok/@fatoumataofficial_.
Asali: TikTok

Matar ta tashi sannan ta taya budurwar da ke taka rawa a filin rawa rausayawa. Yayin da suke rawa tare, sai ta yaba kyawun matashiyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, a hankali ta tambayeta ko tana son danta. Koda dai ba a nuno dan matar a cikin bidiyon ba, @fatoumataofficial_ ta yi martani a TikTok cewa tambayar ta bata mamaki fiye da tunani.

A wani bidiyo daban, matashiyar ta ce bata san matar ba kuma cewa bayan taron, wasu yan uwan matar sun tuntube ta.

Ta ce sun bayyana karara cewa dan matar ya yi mata kankanta. Tana martani ne ga wadanda suka ce suna son ganin matashin da ake magana a kansa.

Jama'a sun yi tururuwan zuwa sashin sharhi don jinjinawa matar, cewa ta nuna kwarin gwiwa.

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

"Ban yi danasani ba": Budurwa ta kashe miliyan 1.9 kan turaruka, bidiyon ya girgiza intanet

Jama'a sun yi martani

@Pink_privacy ta ce:

"Babi, da ta sameni amma ba a iyawa iyaye mata na Afrika, ta ga wani abu da take so ne."

@neoheaux ta ce:

"Tana dariya, amma da gaske take."

@P!n€App!€ ta ce:

"Shin ni kadai ce nake tunanin wannan abun ya yi kyau?"

@ISATU ta ce:

"Don Allah, ina fatan yaron irin wanda kike so ne saboda wannan zai zamo kyakkyawan labari."

@here4fun351 ta ce:

"Idan wata uwa ta yi mani magana haka nan take zan san cewa aurena zai yi karko."

Ango ya fasa aure ana gab da biki

A wani labarin, mun ji cewa wasu iyali a kauyen Sokyot, gudunmar Kipkaren da ke mazabar Mosop, Nandi sun samu karayar zuciya bayan angon diyarsu ya fasa aurensu ana gab da biki.

Da take zantawa da kafar labarai ta kasar Kenya, TUKO.co.ke, wata yar kauyen su amaryar ta bayyana cewa masoyan sun shirya gudanar da shagalin kafin bikinsu a ranar 22 ga watan Disamba, amma hakan bai samu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel