“Ina Aikin Awa Guda Kullun”: Wani Mutum Ya Samu N61.7m Kan YouTube da Bidiyo Daya Kacal

“Ina Aikin Awa Guda Kullun”: Wani Mutum Ya Samu N61.7m Kan YouTube da Bidiyo Daya Kacal

  • Wani mai amfani da Youtube ya samu kudi dala $68,837.78 kan wani bidiyo daya da ya daura a shafinsa na YouTube
  • A wani bidiyo da ya yada a TikTok, mutumin ya ce awa daya kacal yake warewa a kullun don kula da shafinsa na YouTube
  • Ya ce wani bidiyo da ya samu mutum miliyan 9.5 da suka kalla ya sama masa kudi wanda ya kai kimanin naira miliyan 61.7

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani mai amfani da tashar YouTube ya bayyana yadda ake samun riba a dandalin yayin da ya samu kudi naira miliyan 61.7 da daya daga cikin bidiyoyinsa.

A wata wallafa da ya yi a TikTok da shafinsa na, @studiohacksnow, mutumin ya ce ya samu masu kallp miliyan 9.5 da suka kalli daya daga cikin bidiyoyinsa.

Kara karanta wannan

Wani mutum da ke burin gina gida ya dinka riga da buhun simintin Dangote bayan ya mallaki fili 1

Ya samu miliyoyi kan YouTube
“Ina Aikin Awa Guda Kullun”: Wani Mutum Ya Samu N61.7m Kan YouTube da Bidiyo Daya Kacal Hoto: TikTok/@studiohacksnow and Getty Images/ppart.
Asali: UGC

Samun kudi a YouTube

A cewarsa, kiyasin kudaden shiga da za a samu daga wannan faifan bidiyo bai yi kasa da dala 68,837.78 ba, wanda ya kai kimanin naira miliyan 61.7.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana karara cewa awa daya kacal yake dauka a kullun don aiki kan shafinsa na YouTube.

Wasu mutane sun yi watsi da ikirarinsa, amma sai ya nuna shafin YouTube din nasa don tabbatar da ikirarin nasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Helios ta tambaya:

"Tallace-tallace nawa ne a cikin kowani bidiyo?"

@Mario Spiroglou ya ce:

"Wannan abin ban mamaki ne."

@Jose David Chavez ya ce:

"Ahafukan da ke yaren Turanci ne kawai za su iya samun irin wadannan masu kallo."

@Lavvy ta ce:

"Toh, amma ta yaya za a samu masu kallon?"

Yadda ake samun arziki a turai

Kara karanta wannan

"Ya hadu": Wani mai zanen gida ya kafa tarihi, ya gina zagayayyen gida a kauyensa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mazaunin New Brunswick ya yi bayanin yadda baki za su iya samun makudan kudade a Canada.

A wani bidiyo mai tsawon mintuna 9 a TikTok, dan Najeriyan ya shawarci jama'a da su daina tura kudi gida don gina masu gidaje.

Ya ce mataki na farko shine fara tara kudi don mutum ya iya siyan fili ko filaye, yana mai cewa akwai yankunan da za su iya samunsu a arha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel