Kudi Masu Gidan Rana: Bidiyon Lefen Alfarma da Aka Kai Wa Amaryar Dan Sani Abacha Ya Girgiza Intanet

Kudi Masu Gidan Rana: Bidiyon Lefen Alfarma da Aka Kai Wa Amaryar Dan Sani Abacha Ya Girgiza Intanet

  • Mustapha Sani Abacha, dan marigayi tsohon Shugaban Kasa Sani Abacha ya angwance da kyakkyawar amaryarsa
  • An daura auren Mustapha da Safa Tijjani Saleh Geidam a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, a garin Maiduguri
  • Kayan lefe da aka hadawa amaryar ya tashi kan mutane da dama a dandalin soshiyal midiya bayan bayyanan bidiyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ana shagulgulan biki a gidan tsohon shugaban kasa, marigayi Sani Abacha inda dansa, Mustapha Sani Abacha ke angwancewa.

A ranar Asabar, 23 ga watan Disamba ne dandazon jama'a suka shaida daurin aure tsakanin Mustapha da kyakkyawar amaryarsa, Safa Tijjani Saleh Geidam a masallacin Mohammed Ali da ke garin Maiduguri, jihar Borno.

Mustapha Abacha da amaryarsa Safa Tijjani
Kudi Masu Gidan Rana: Bidiyon Lefen Alfarma da Aka Kaiwa Amaryar Dan Sani Abacha Ya Girgiza Intanet Hoto: weddings_and_cruise
Asali: Instagram

Kamar yadda yake bisa al'adar Mallam Bahaushe da yan arewa, yan uwan ango su kan taru su kai akwatuna da kayayyaki gidan amarya da sunan kayan lefe.

Kara karanta wannan

Hotuna sun bayyana yayin da Shettima, gwamnoni suka halarci daurin auren dan Abacha a Maiduguri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ce ta kasance a bangaren iyalin tsohon shugaban kasar inda aka kwashi akwatunan alfarma saiti-saiti zuwa gidan su amaryar Safa.

Yawan akwatuna da kayayyakin da dangin ango Mustapha suka kai gidanm amaryarsa ya girgiza al'umma yayin da bidiyo ya bayyana a dandalin soshiyal midiya.

Mutane da dama sun mato a kan kayan lefen da aka hada inda suka taya amarya murnar cewa lallai ta yi goshi.

Kalli bidiyon lefen a kasa:

Martanin jama'a kan kayan lefen

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a yayin da shafin fashionseriesng ya wallafa bidiyon lefen a dandalin Instagram.

maryama5163 ta yi martani:

"Masha Allah, masu kudi kam sun more abunsu, wasu lokutan na kan yi mamakin yadda mutane ke tara kudi, ina ta kokarin hada 50k tun farkon shekarar nan ga shi har ya kusa karewa ban cimma nasarar siyan keken dinki ba domin samun hanyar tara kudaden shiga don duba yarana, ni bazawara ce da mijinta ya mutu, masha Allah amarya kam tayi goshi Allahumma arzuqnee."

Kara karanta wannan

“Na kashe shi ne saboda ya hana ni kashe kaina”: Matar da ake zargi da kashe abokin mijinta a Kano

yakaka27kalli ta yi martani:

"Wannan kususuram ne ba lefe ba ."

dolcezza__oven ta ce:

"Masha Allah …Allah ya sanya Alkhairi."

zuzus_collectionss ta yi martani:

"Masha Allah tabarakallah Allah ya Sanya alkairi ."

chopsmanor_ ta ce:

"Don Allah ku kirga min na rude na kasa yi."

natural_supplements_ ta ce:

"@khadeey_ masha Allah. aikin ki yayi kyau."

Shettima, gwamnoni sun halarci daurin aure

A baya mun kawo cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci daurin auren dan marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha, Mustapha Sani Abacha.

Wasu gwamnoni da suka hada da na gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, takwaransa na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf duk sun samu halartan daurin auren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel