Wata Attajirar Mata Ta Gwangwaje Yan Biki da Tukunyar Gas, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Wata Attajirar Mata Ta Gwangwaje Yan Biki da Tukunyar Gas, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • A wajen bikin karshen shekara, wata attajirar mata ta gwamgwaje bakinta inda ta yi masu kyautar tukunyar gas
  • An gano matar tana mikawa wadanda suka halarci taron tukunyar gas, inda su kuma suka karba cike da farin ciki da annashuwa
  • Wata mata da rabon bai kai kanta ba ta tunkari uwar bikin inda ta mallaka mata nata kason

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Bakin da suka halarci taron karshen shekara da wata attajirar mata yar Najeriya ta shirya sun kwashi garabasa mai tsoka.

Jama'a sun cika da mamaki lokacin da aka ga uwar taron tana ta rabawa wadanda suka halarci taron tukunyar gas daya bayan daya, inda su kuma suka dungi yi mata godiya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da fursunoni 3 suka tsere daga gidan gyaran hali na Ogun, an fara farautarsu

Wata mata ta raba tukunyar gas a wajen biki
Wata Attajirar Mata Ta Gwangwaje Yan Biki da Tukunyar Gas, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @oyinlola5/TikTok
Asali: TikTok

Wata mata da rabon bai kai kanta ba da farko ta tunkari matar mai cike da karamci don roko nata. Dauke da murmushi a fuskarta, uwar gayyar ta ba ta tabbacin cewa ta tanadi isasshen tukunyar gas din domin ya kai kan kowa. Sannan ta mika mata nata yayin da suka rungumi juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Olabode09 ya yi martani:

"Wai tukunyar gas din wasan yara ko dai na gaske."

Chrismotik ya ce:

"Shakka babu wannan ankon zai kai 80-100k."

Shuga ta rubuta:

"Babu biki da ya yi kamar na Yarbawa wasi saura za su ci gaba da koyo ne."

Queen g Esther:

"Ku tambayi nawa suka siya anko."

User5166296272076:

"Idan suka siyar da kaya 150k toh me zai hana su raba buhun shinkafa."

Balogunhikmat0125:

"Ina a wajen bikin nan, wannan tukunyar gas da suka raba, akwai fa gas a ciki,"

Kara karanta wannan

"Na shafe tsawon watanni ina zawarcinsa", Aisha Yesufu ta magantu kan yadda suka hadu da mijinta

Hopeorebela:

"Wannan leshi ne da ake siyarwa 25k aka bayar kan 40k,,,,Me zai hana su raba tukunyar gas."

Saratumuhammad563:

"Ni bahaushiya ce amma wallahi ina kaunar Yarbawa."

Matashi ya fasa asusun bankinsa

A wani labarin, mun ji cewa wani bidiyo da ke nuno wani mutum da ke fasa asusunsa na katako tare da fito da takardun kudade da suka hada da KSh 1000 da KSh 500 ya ba mutane da dama mamaki.

Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba ya shiga gasar nan na yan Kenya da ke nuna yawan kudaden da suka tara a gida tsawon shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel