“Ya Hadu”: Wani Mai Zanen Gida Ya Kafa Tarihi, Ya Gina Zagayayyen Gida a Kauyensa

“Ya Hadu”: Wani Mai Zanen Gida Ya Kafa Tarihi, Ya Gina Zagayayyen Gida a Kauyensa

  • Wani dan Najeriya da ke aikin zana gida ya zama zakaran gwajin dafi a kauyensa sakamakon yadda ya nuna lallai shi kwararre ne a bangaren gini
  • Diyarsa da ke cike da alfahari ta garzaya soshiyal midiya don baje kolin zagayayyen gidan da mahaifinta ya ginawa kansa a kauyen
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyonta mai ban mamaki sun yaba tsarin gidan tare da jinjinawa wanda ya kera shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani dan Najeriya da ke aikin zana gini ya dauka hankalin jama'a kan wani zagayayyen gida da ya kerawa kansa a kauyensu.

Aikin ginin nasa ya dauka hankali ne bayan diyarsa, @sharonoreoluwa__, ta baje kolinsa a dandalin TikTok.

Kara karanta wannan

Maganar aure na rawa bayan saurayi ya sa budurwa ta girkawa danginsa su 70 abinci, gishiri ya zarce

Hadadden gida na alfarma
An yi amfani da hoton mutumin don misali ne Hoto: (sharonoreoluwa_), Maskot
Asali: TikTok

@sharonoreoluwa__ da ke cike da alfahari ta rubuta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina kaunar gidan nan sosai, ya matukar haduwa da kyau."

Haifaffiyar yar jihar Ekitin ta nunawa kewayen wajen gidan, wanda ya burge mutane da mamaki.

Bidiyon nata na TikTok ya ja hankalin mutum fiye da 124k da suka kalla a daidai lokacin kawo wannan rahoton. Sai dai ba a san dalilin mahaifinta na zabar irin wannan zagayayyen gida ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Pascal ya ce:

"Ina so na aure ki don na girbe a wurin da ban shuka ba."

Moyomoluwa Falade ta ce:

"Kawuna da ke aikin zana gini ya kera gidansa kamar jirgin Annabi Nuhu."

Essie ta ce:

"Gaskiya gidan ya yi daban kuma yana da kyau."

Kelly ta ce:

"Gaba daya sai tashin kanmu kuke yi da gida."

Kara karanta wannan

Za mu shawo kan dukkan matsaloli tare da karfafa Najeriya - Ganduje

Fx Daniel Savage ya ce:

"Wato dai mahaifina ne kawai bai da gida a kauye Allah ya kyauta."

Susan d Chubbyfarmgirl ta ce:

"Don Allah ki fada ma baba yana bukatar shuke-shuke kewaye da wannan hadadden gida."

Matashi ya kera katafaren gida

A wani labarin, mun ji cewa bidiyon wani matashi da ya fita daga talaucinsa tare da cimma mafarkinsa na gina katafaren gida nasa na kansa ya taba zukatan mutane da dama.

Bidiyon ya nuno sauyawar da ya yi na ban mamaki daga mai tuka babur da ke fama da rayuwa zuwa shahararren dan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel