Wani Mutum Da Ke Burin Gina Gida Ya Dinka Riga da Buhun Simintin Dangote Bayan Ya Mallaki Fili 1

Wani Mutum Da Ke Burin Gina Gida Ya Dinka Riga da Buhun Simintin Dangote Bayan Ya Mallaki Fili 1

  • Wani dan Najeriya ya haddasa cece-kuce bayan ya yi amfani da buhun simintin Dangote wajen dinkawa kansa da abokansa riga
  • Mutumin ya sanya rigar ya shiga jama'a yayin da yake addu'ar cewa wata rana zai yi arzikin da zai mallaki gida nasa na kansa
  • A cewarsa, ya yi nasarar mallakar fili a 2023, jawabin da yasa mutane da dama tunanin ko Aliko Dangote zai taimaka masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani matashi dan Najeriya wanda ya dade yana mafarkin gina gida ya sanya kaya na musamman da ya dinka da buhun simintin Dangote.

Shi da abokansa sun sanya tufafin yayin da yake magana kan burinsa na mallakar gida wata rana.

Matasa sanye da rigar simintin Dangote
Wani Mutum Da Ke Burin Gina Gida Ya Dinka Riga da Buhun Simintin Dangote Bayan Ya Mallaki Fili 1 Hoto: @officialfowobi
Asali: TikTok

Simintin Dangote na gini

Kara karanta wannan

"Ya hadu": Wani mai zanen gida ya kafa tarihi, ya gina zagayayyen gida a kauyensa

Mutumin ya bayyana cewa yana matukar farin ciki saboda ya siya fili a 2023 kuma ya yi nasarar yin yar shinke a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ya yi amfani da simintin Dangote wajen gina shingen a kan filinsa. Ya yi addu'ar mallakar gida nasa na kansa wata rana.

Mutane da dama sun bayyana cewa lallai telan nasa ya yi kokari sosai wajen dinka masa wannan riga. @officialfowobi ya yada bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

icon ya ce:

"Mutane da ke da lafiya a kasar nan basu kai 10."

Micolax ya ce:

"Magana ta gaskiya telan da ya dinka kayan nan ya san aiki fiye da tela na."

Tunji Atitebi ya ce:

"Hmmmm wannan ya yi ma'ana Allah ya albarkacesu su duka."

Sapphiretunez ya ce:

"Me yasa basu goge shi ba."

Kara karanta wannan

Maganar aure na rawa bayan saurayi ya sa budurwa ta girkawa danginsa su 70 abinci, gishiri ya zarce

Ope MaLLY ya ce:

"Duk wannan da kuke yi, bai shafi Dangote."

Tossing1 ya ce:

"Siminti ya yi tsada don haka dole mutum ya yi amfani da komai na shi. Tunani mai kyau."

Magidanci ya kera hadadden gida

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dan Najeriya da ke aikin zana gini ya dauka hankalin jama'a kan wani zagayayyen gida da ya kerawa kansa a kauyensu.

Aikin ginin nasa ya dauka hankali ne bayan diyarsa, @sharonoreoluwa__, ta baje kolinsa a dandalin TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel