“Na Rasa Abokai da Yawa Saboda Auren” : Matashi Ya Yi Wuff da Tsala-Tsalan Yan Mata 2 a Rana 1

“Na Rasa Abokai da Yawa Saboda Auren” : Matashi Ya Yi Wuff da Tsala-Tsalan Yan Mata 2 a Rana 1

  • Wani fitaccen matashi dan kasar Ghana, Godfada GH Houston, ya yi wuff da kyawawan yan mata biyu a rana daya
  • Jama'a sun caccaki Houston bayan aurensa da matan nasa biyu wato Felicity da Khadijah, a wani kasaitaccen biki da ya dauka hankali
  • Angon ya bayyana cewa ya rasa abokai da dama saboda matakin da ya dauka na auren mata biyu a lokaci guda

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani fitaccen mai watsa shirye-shirye dan kasar Ghana, Michael Houston, wanda ya sha caccaka saboda auren mata biyu a rana daya, ya kare kansa yayin da ya bayyana illar da hakan ya janyo masa.

A kwanan nan ne Houston ya auri Felicity da Khadijah a wani gagarumin biki da aka gudanar, inda hakan ya janyo masa shan caccaka a wajen mutane.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi halin da ake ciki a bincike kan jefa Bam a taron Musulmai a Kaduna

Matashi ya auri mata biyu a rana daya
“Na Rasa Abokai da Yawa Saboda Auren” : Matashi Ya Yi Waff da Tsala-Tsalan Yan Mata 2 a Rana 1 Hoto: Michael Houston
Asali: Facebook

"Bana neman yardar kowa don auren mata biyu" -Houston

Da yake karin haske kan lamarin, Houston ya garzaya shafinsa na Facebook a ranar Laraba domin kare kansa kan wannan aure da ya yi, yana mai cewa ya rasa abokansa da dama saboda wannan abu da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"Saboda mabiyana da ke waje, zan yi dan bayani. Na auri wadannan kyawawan mata guda biyu, Adepa Fel Houston da Deejah Houston, sai kuma kasar ta dauki dumi saboda mutane ba su fahimci yadda na sa hakan ta faru ba, inda mutane da yawa suka yi ta ba'a ga lamarin gaba daya.
"Wato, abin da ba ku sani ba shi ne, na yi baiko guda biyu a kowani bangare, kuma an yi duk wasu abubuwan al'ada na aure har zuwa karshe. Mun yi dan kwarya-kwaryan bukukuwa inda malaman addini suka sanya albarka a auren.

Kara karanta wannan

Mu leka kotu: Dan kasuwa ya nemi naira miliyan 1 daga hannun matarsa kafin ya sake ta

"Sai na yanke shawarar yin wani kasaitaccen biki wanda na sanar da duniya cewa Allah ya albarkaci gidana da sarauniya har biyu.4
"Ban sani ba ashe wannan zai sa ayi mani lakabi da wanta baya mutunta mata. Ta yaya zan kashe dukiya don in wulakanta mata ta hanyar aurensu?"

Matashin ya kara da cewar, wannan matakin da ya dauka na auren mata biyu yasa abokansa da dama sun guje shi sannan kuma cewa ya kara yin wasu abokan bayan nan.

Ya kara nanata cewa yana da abun da zai iya kula da matansa biyu tare da sanya su farin ciki don haka baya neman amincewar kowa. A cewarsa zabinsu ne auren.

Matashi ya sace zuciyar budurwa a Twitter

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa shekaru biyu baya, wani matashi dan Najeriya ya ci karo da shafin wata mata a Twitter kuma nan take kyawunta ya dauki hankalinsa.

Sai ya yanke shawarar aika mata da sako a twitter, amma ba wai kowani irin rubutu ba. Ya so ya sanya ta dariya da kuma jan hankalinta, don haka sai ya aika mata sako mai ban dariya da ke nuna aniyarsa na son aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel