Kyakkyawar Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Samun Kyautar N20k Don Ta Biya Kudin Makaranta

Kyakkyawar Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Samun Kyautar N20k Don Ta Biya Kudin Makaranta

  • Wata kyakykyawar daliba ta fashe da kuka a lokacin da wani bakon matashi ya ba ta kyautar naira dubu 20
  • Kafin matashin ya ba ta kudin, Saubirin ta yi magana game da abubuwan da take so ta yi a rayuwata idan ta sami dama
  • Mutane da yawa da suka ga yadda dalibar ta ji dadi sun ce ita mace ce mai yawan godiya kuma ta cancanci kowane taimako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani kwararren mai daukar hoto wanda ke tallafa wa mutane idan ya hadu da su, ya shiga cikin wata makaranta, inda ya hadu da wata kyakkyawar budurwa.

Mai daukar hoton @austinebbs ya dauki hoton budurwar ba tare da saninta ba, inda ya je gareta don ya nuna mata, sun tattauna kan batutuwan da suka shafi rayuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dawo da shirin ciyar da yan makaranta abinci kyauta da gwamnatin Buhari ta fara

Budurwa ta fashe da kuka bayan samun kyautar N20k
Kyakykyawar daliba ta fashe da kuka a lokacin da wani bakon matashi ya ba ta kyautar naira dubu 20 Hoto: @austinebbs
Asali: TikTok

Kyakkyawar daliba ta samu kyautar N20k don biyan kudin makaranta

Budurwar mai suna Saubirin, ta ce tana da burin zama mai daukar hoto da kuma zama tauraruwa a masana'antar tallace tallace, amma da alama mafarkinta ba zai cika ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalibar ta ce tana sayar da cincin a cikin makarantar don ta tara kudin da za ta taimaki kanta. Ko da matashin ya yi mata hoto, ta yi mamaki matuka.

Matashin ya ba Saubirin kyautar naira dubu ashirin don kari kan wanda take tarawa, ta fashe da kuka, inda ta bayyana cewa ta jima tana tunanin hanyar samun kudin makarantarta.

Kalli bidiyon budurwar a kasa:

Budurwa ta nuna wa 'yan Najeriya yadda za su je Norway a saukake

A wani labarin, wata matashiya ta shawarci mutane kan yadda ake samun biza zuwa kasar Norway da kuma yadda mutum zai yi kaura zuwa kasar ta Schengen.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Saurayi ya kashe budurwarsa bayan ta nemi ya biya ta kudin gamsar da shi

Mai ba da shawara kan tafiye-tafiyen, Grandma Shasha, ta lura cewa biza zuwa Norway yana kai kusan naira 72,000 ne kawai a kudin Najeriya.

A cewar ofishin jakadancin Norway a Najeriya, takardar bizar baki da ta kai Yuro dubu 72, tana ba mai ita damar zama a Norway ko wasu kasashe na yankin Schengen na tsawon kwanaki 90 a cikin kwanaki 180.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel