Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Gwamnatin jihar Kano ta dage cewa Muhammadu Sanusi II shi ne dai Sarkin Kano, bayan hukuncin da wata kotu ta yanke a ranar Alhamis kan dokar rusa masarautun jihar.
Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinan 'yan sanda, Hussaini Gumel ya fitar da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nasarawa a jihar Kano.
Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan dambarwar masarautun jihar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.
An fara shiga fargaba a Kano bayan da Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan halaccin dokar da ta rusa masarautun jihar guda biyar da kuma nadin Sanusi II.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yi wats da dokar da majalisar dokokin Kano ta yi amfani da ita wajen nada Muhammadu Sanusi II sarkin Kano.
Dokar majalisar masarautar Kano ta 2024, wacce ta rusa masarautun jihar guda biyar na nan daram amma kotu ta lalata matakan da gwamnan ya dauka na aiwatar da dokar.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sanar da cewa za ta ci gaba da zaman shari'ar kan rigimar sarautar Kano da misalin karfe 2:00 na rana yau Alhamis.
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta sanar da mutuwar wani mutum guda daya tare da jikkata jami'anta biyu yayin da ake tsaka da shari'ar sarautar Kano.
Majasar dokokin jihar Kano ta ɗaukaka ƙara kan dokar masarauta wadda ta saukw sarakuna biyar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya naɗa a lokacin mulkinsa.
Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Samu kari