Kotu Ta Yi Magana Yayin da Ake Jiran Yanke Hukunci Kan Sahihancin Tube Sarkin Kano

Kotu Ta Yi Magana Yayin da Ake Jiran Yanke Hukunci Kan Sahihancin Tube Sarkin Kano

  • An samu jinkirin yanke hukunci kan sahihancin sabuwar dokar masarautar Kano wadda ta sauke sarakuna biyar kuma ta mayar da Sanusi II
  • Magatakardar Babban Kotun Tarayya mai zama a Kano ya sanar da ɗage zaman yanke hukuncin zuwa ƙarfe 2:00 na tsakar rana yau Alhamis
  • Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗanagundi ne ya shigar da ƙarar yana kalubalantar sahihancin dokar da ta sauke Aminu Ado

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa za a ɗan samu jinkirin yanke hukunci kan sahihancin dokar masarautar Kano 2024 da ta tube sarakuna biyar.

Yayin da mutane ke dakon jin wane hukunci babbar kotun tarayya za ta yanke, an ɗage zaman zuwa ƙarfe 2:00 na rana yau Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: An fara zaman ɗari ɗari a Kano bayan hukuncin da kotu ta yanke

Muhammadu Sanusi da Aminu Bayero.
Kotu ta dage yanke hukunci a shari'ar masarautar Kano zuwa karfe 2:00 na rana Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, sabuwar dokar da majalisar dokokin Kano ta amince da ita a watan Mayu, ta jawo rigima bayan Gwamna Abba Kabir ya rattaɓa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da sabuwar dokar ta ƙunsa

Sabuwar dokar ta kai ga tsige Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, tare da rusa sababbin masarautu hudu da Ganduje ya kirkiro da suka hada da Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

Har ila yau dokar ta kuma mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar sarauta a matsayin Sarki na 16, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Babba, ya kalubalanci halaccin wannan sabuwar doka a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Kano.

Tsagin Aminu Bayero sun kai ƙara kotu

Danagundi ta hannun lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN), ya roki kotu da ta soke dokar, ma'ana ta tabbatar da Aminu Ado Bayero a matsayin halattaccen Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan dambarwar masarautar Kano

Bayan sauraron ƙorafin ranar Juma’ar da ta gabata, Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya dage shari’ar zuwa yau Alhamis.

A halin yanzu an dage zaman kotun da safiyar Alhamis din nan zuwa karfe 2:00 na rana kamar yadda magatakardan kotun ya sanar.

Yan sanda sun nemi a zauna lafiya

A wani rahoton rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta roƙi jama'a su zauna lafiya a lokacin da ake dakon hukuncin Babban Kotun Tarayya kan rigimar sarauta.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan Kano , SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano ranar Alhamis.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262