Jam'iyyar PDP
Yusuf Kibiya ya samu goyon bayan mafi yawan jagororin jam'iyyar PDP a jihar Kano, inda ya samu nasara a kan abokan takararsa da suka hada da Nura Nuhu da Sani Aliyu.
Shugabannin jam'iyyar APC a gundumar Toru-Ndoro da ke karamar hukumar Ekeremor a jihar Bayelsa sun dakatar da shugaban APC, Mr Eniekenemi Mitin daga mukaminsa.
PDP ta kammala shirin kashe wutar rikicin shugabanci a karshen Oktoban nan. majalisar NEC za ta sauke daukacin shugabannin jam’iyyar PDP kafin labari ya canza.
Tsohon gwamnan Ekiti bai da matsala idan rikicin cikin gidan jam’iyyar adawa ta PDP ta kashe kowa. Ayo Fayose ya koma ‘dan kallo yayin da ake yaki a jam'iyya.
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose mai suna Isaac Fayose ya ce daga yau shi ne shugaban PDP inda ya ce duk wanda ba yarda ba ya je kotu yana jiransa a can.
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum, ya yi wa wadanda suka siyar da kuri'unsu a lokacin zaben 2023 shagube kan tsadar rayuwa.
An gano gaskiya kan ikirarin da aka yi na cewa Atiku Abubakar ya bayyana goyon bayansu ga gwamnan Bauchi a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2027
Jam'iyyar APC reshen jihar Bayelsa ta sanar da dakatar da karamin Ministan mai, Heineken Lokpobiri da tsohon dan takarar gwamna, David Lyon a yau Juma'a.
APC ta ce yan kasa na ganin sauyi mai ma'ana a Najeriya a karkashin mulkin Bola Tinubu saboda haka babu bukatar neman sauyi kamar yadda PDP ta bukata.
Jam'iyyar PDP
Samu kari