Jam'iyyar PDP
Kungiyar MURIC ta kare Sanata Shehu Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu kan zargin daukar nauyin ta'addanci inda ta yi Allah wadai da kazafin da aka yi masa.
Rahotanni sun bankado yadda aka yi yarjejeniya da APC ta yi nasara a karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom domin shirin Gwamna Umo Eno kan zaben 2027.
Kotun daukaka kara ta tumbuke dan majalisar wakilai kan magudin zabe. Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilan PDP ta ba dan LP nasara bayan gano magudi.
Jigon APC, Tonye Cole ya ce dole ne Wike, Fubara, Amaechi, Odili Dole su ajiye bambancin siyasa su magance tashe tashen hankula da suka addabi jihar Ribas.
An samu sabani a wani taro da PDP ta gudanar a Abuja. Shugabannin jam'iyyar sun yi arangama kan wanda ya haddasa rikicin da ya mamaye su tsakanin Wike da Atiku.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya shawarci Gwamna Siminalayi Fubara ya bi umarnin kotu domin a samu zaman lafiya a jihar Rivers.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya dora alhakin rikicin jihar Rivers a kan Gwamna Siminalayi Fubara. Wike ya ce gwamnan ba ya bin umarnin kotu.
Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya roki Ministan Abuja kuma tsohon uban gidansa, Nyesom Wike kan samuwar zaman lafiya a jihar, amma ya ce hakansa bai cimma ruwa ba.
Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna damuwa kan martanin da Shugaba Bola Tinubu ya yi game da rikicin jihar Rivers inda shugaban ya kira sunansa shi kadai.
Jam'iyyar PDP
Samu kari