Rikicin PDP
A kokarin warware rigimar siyasar jihar Ribas, ƴan majalisar amintattu BoT na jam'iyyar PDP sun gana da Nyesom Wike a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce jiharss na da wadataccen ruwan da zai kashe kowace irin wuta, ya ce watakila ya faɗi wasu kalamai da suka ɓata ran Wike.
Shugaban jam'iyyar PDP na yanzu ya bayyana alakar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Rivers da kuma tasirinsa ga zaben da aka gudanar bara.
Ana saura kwanaki bakwai a gudanar da zaben jihar Edo, tsohon Sanatan Edo ta Arewa, Francis Alimikhena ya watsar da PDP inda ya koma jam'iyyar APC.
Umar Iliya Damagum ya ce babu wata jam’iyya mafi girma a kaf nahiyar Afrika PDP. Ambasada Umar Iliya Damagum ya ce an kawo APC, NNPP da LP ne domin cin zabe.
Jam’iyyar PDP ta fallasa abubuwan da INEC ta yi a zabukan 2015 zuwa 2023. Umar Iliya Damagum ya zargi hukumar INEC da murde zabukan da aka yi a 2019 da 2023.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake fitowa ya nuna yatsa ga gwamnonin jam'iyyar PDP. Wike ya ce bai ci amanar jam'iyyar ba.
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya caccaki Gwamna Siminalayi Fubara kan karairayi da yake yi masa bayan mara masa baya.
Kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa ya zauna taro jiya Alhamis a birnin Abuja ƙarƙashin muƙaddashin shugaba, Umar Damagum. An amince da gangamin Rivers.
Rikicin PDP
Samu kari