Jihar Oyo
A watan Yulin 2025, sarakuna uku daga jihohi daban daban a Najeriya sun riga mu gidan gaskiya, ɗaya daga ciki shi ne Sarkin Gusau, Ibrahim Bello.
PDP za ta gudanar da babban taronta a Ibadan daga 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. Ta dauki matakin doka kan mambobin da suka sauya sheka bayan lashe zaɓe.
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Oyo, Rt. Hon. Adebo Ogundoyin ya yi alhinin rasuwar babban limamin Oruwa, Sheikh AbdulKareem Olore, ya roki Allah Ya gafarta masa.
Tanka dauke da lita 33,000 na man fetur ta fashe a Celica, Ibadan, kusa da gidan man NNPCL bayan ta yi karo da mota sakamakon shanyewar birki, gobara ta tashi.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa ko kaɗan tafiyar Atiku Abubakar ba zai wa PDP illa ba, yana mai cewa jam'iyyar tana nan da ƙarfi da farin jininta.
Jihar Oyo za ta kashe N7.7bn don siyan jiragen yaki guda biyu da za su taimaka wa Amotekun da jami'an tsaro wajen yaki da masu garkuwa da mutane.
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya bayan mulkinsa na shekara guda, ya bar gadon zaman lafiya da ci gaba a Ibadan.
An yi babban rashi a jihar Oyo bayan rasuwar daya daga cikin manyan sarakunan da ake ji da su. Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu.
Yayin ake tunkarar sabuwar shekarar Musulunci, Gwamna Seyi Makinde ya ayyana Juma’a, 27 ga Yunin 2025 a matsayin hutun ma'aikata a fadin jihar Oyo.
Jihar Oyo
Samu kari