Jami'o'in Najeriya
Akhaji Aliko Dangote ya dauki nauyin yin ayyuka guda 7 a jami'ar kimiyya da fasaha da ke karamar hukumar Wudil a jihar Kano. Farfesa Musa Yakasai ne ya sanar.
Jami'ar Bayero da ke jihar Kano ta sanar da korar dalibai 29 bisa samunsu da laifin satar amsa yayin jarrabawa, jami'ar ta dakatar dalibai 3, ta gargadin guda 15.
Jami’ar jihar Kwara ta kori dalibai 175 bisa laifuffukan da suka hada da satar jarrabawa, cin zarafi, damfara, shiga haramtattun kungiyoyi da mallakar bindiga.
Hukumar kula da asusun bayar da lamunin karatu ta kasa (NELFUND) ta bayyana cewa dalibai daga makarantu mallakar jihohin kasar nan 36 za su samu lamunin karatu.
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin Kano Electric (KEDCO) ya maido da wutar lantarki a jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, bayan an biya shi Naira miliyan 100.
Kungiyar ma'aikatan jami'a ta kasa SSANU na shirin tsunduma yajin aiki a gobe Alhamis. Hakan ya biyo bayan wa'adin mako biyu da kungiyar ta ba gwamnati ne.
Hukumar kula da asusun ba dalibai rancen kudin karatu NELFund ta ce ana sa ran daliban kasar nan akalla 250,000 zuwa 300,000 ne za su nemi lamunin karatu.
'Yan bindiga sun kai hari gidan wani malamin jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke Katsina. An ce 'yan ta'addan sun kashe malamin, sun kuma tafi da yaransa biyu.
Ministan Ilimi a Najeriya, Farfesa Tahir Mamman ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu su yi koyi da Dakta Emeka Offor wajen tallafawa harkar ilimi a Najeriya.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari