Bayan Rasa Mulkin Kano, a Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Nasiru Gawuna Mukami

Bayan Rasa Mulkin Kano, a Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Nasiru Gawuna Mukami

  • A karshe, dan takarar gwamnan a jihar Kano a karkashin jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya samu mukami
  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Alhaji Gawuna shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Bayero da ke jihar Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan sauye-sauye a mukaman da ya yi a kwanakin baya wanda babu sunan Gawuna a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada Nasiru Yusuf Gawuna babban mukami a Jami'ar Bayero da ke jihar Kano.

Tinubu ya nada Gawuna muƙamin shugaban kwamitin gudanarwar na Jami'ar bayan sake yin garambawul a mukaman.

Tinubu ya ba Gawuna mukami a Jami'ar Bayero
Bola Tinubu ya naɗa Nasiru Gawuna muƙamin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Bayero Kano. Hoto: Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Kano: Mambobin kwamitin da Gawuna zai jagoranta

Sauran ƴan kwamitim da ke karkashin Gawuna sun hada da Abubakar Dauda da Nora Alo da Ibrahim Obanikoro da kuma Musa Abbas, cewar NTA News.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC ya fallasa wanda ya jawo ake binciken gwamnatin El-Rufai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin nadin Gawuna, tsohon Ministan Kasafi da tsare-tsare, Udoma Udo Udoma shi ne aka nada shugaban kwamitin na Jami'ar Bayero, Punch ta tattaro.

Daga cikin mambobin kwamitin a wancan lokaci akwai Farfesa Idris Nasiru Maiduguri Farfesa Uchenna Newi da Salisu Mohammed Birniwa da kuma Fola Akinsete.

Tinubu ya yi nadin mukaman ne a ranar 18 ga watan Mayun wannan shekara ta 2024 da muke ciki, wanda ya kai mutane 555.

Gawuna ya yi rashin nasara a kotu

Wannan nadin na Nasiru Gawuna na zuwa ne bayan shan kaye a Kotun Koli kan shari'ar zaben Kano.

Tun farko ɗan takarar APC ya yi nasara a kotun sauraran ƙararrakin zabe da kuma Kotun Daukaka Kara.

Daga bisani, Kotun Koli ta yi fatali da korafe-korafensa inda ta tabbatar da Gwamna Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zabe.

Kara karanta wannan

Ana daf da zaɓe, ƙanin Gwamna ya watsa masa ƙasa a ido, ya bar jam'iyyar PDP

Tinubu ya nada mukamai a manyan makarantu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada mukamai akalla 555 a manyan makarantun Najeriya.

Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmoud Aliyu Shinkafi shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Jos.

Sai kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Yayale Ahmed shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.