Majalisar dattawan Najeriya
Ministan makamashi ya bayyana cewa za a gama gyara wutar Arewa a cin kwanaki 12 masu zuwa, ya ce gyaran wutar Arewa zai dauki mako biyu daga yanzu.
Gwamnan jihar Zamfara ya ce yan majalisun Arewa, Sanatoci da yan majalisar wakilai za su yi watsi da bukatar Bola Tinubu kan sabuwar dokar haraji.
Dan majalisa mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam, Datti Yusuf Umar ya ce lalacewar wutar lantarki a Arewa ya jawo matsaloli da asarar rayuka masu tarin yawa.
Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da cewa an dage shirin tantance sababbin Ministoci da shugaban ya nada da aka shirya yi a yau Talata 29 ga watan Oktoban 2024.
Majalisar dattawa ta fara shirin tantance mutum 7 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin sababbin ministoci bayan ya yi garambawul.
Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje ya musanta cewa an rika watsa kudi a bkin ‘yar sa, Fauziyya Danjuma Goje da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
An kafa kwamiti da zai yi aiki a Majalisa ya yi bincike kan yadda aka dauki ayyuka a wasu hukumomi. Za a gabatar da rahoto a zauren majalisa cikin makonni hudu.
Majalisar wakilan Najeriya ta yi fatali da ƙudurin da ya nemi a yi wa wasu sassa na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 kwaskwarima saboda ya saba da tsarin da kasa.
Sanatoci da dama da suka hada da Yahaya Abdullahi (PDP, Kebbi ta Arewa), sun bayyana damuwarsu kan tsakuro kudaden jihohi domin gudanar da a ayyukan hukumomin.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari