Hukumar yan sandan NAjeriya
Jami'an rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna sun samu nasarar kubutar da mutane 3 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Zariya, jihar Ƙaduna.
Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar gasawa ƴan bindiga aya a hannu a jihar Kaduna. Ƴan sandan sun fatattaki miyagun ƴan bindiga tare ceto mutanen da suka sace.
Wani mashahurin dan damfara ya dauko hayar sojoji don kama wani malamin Musulunci mai suna Sulaimon saboda addu'ar bogi da ya masa bai ci nasara ba a aikinsa.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da fara gudanar da bincike a kan rade-radi da ke yawo na zargin bullar wasu mata masu shiga gidan mutane suna shan jini.
Yayin da ake cikin halin yunwa, ana zargin wani dalibi a makarantar horas da 'yan sanda a Kano ya rasa ransa sakamakon rashin abinci mai gina jiki da wahalhalu.
Kasurgumin dan daba da ake nema ruwa a jallo, Sadiq da aka fi sani da 'Big Star' a Kano ya shiga hannu bayan kama shi ya ji wa wani dattijo rauni da makami.
Rundunar yan sanda reshen jihar Kwara ta yi nasarar damƙe Malamin nam da ta ayyana nemansa ruwa a jallo bisa zargin yi wa mabiya addinin gargajiya barazana.
Wani matashi mai suna Ridwan ya shiga hannun jami'an tsaro bayan an kama shi da zargin kisan mahaifinsa Ishau tare da cire wasu sassa na jikinsa a jihar Ogun.
Jami'an rundunar yan saɓda reshen jihar Legas sun kama wani matashi da ake zargin ya halaka masoyiyarsa saboda tunanin zata guje shi a wata Anguwa a Legas.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari