Hukumar yan sandan NAjeriya
Ƴan bindiga sun tare hanya sun yi awon gaba da limamin cocin Katolika ta Enugu, Rev. Fr. M. Okide, tare da wasu mutum shida da ba su ji ba, ba su gani ba.
Wata kwamishinar harkokin mata a jihar Ondo, Olubunmi Osadahun ta gamu da fushin wani matashi kan zargin nuna wariya na rabon kayan tallafi don rage radadi.
Rundunar yan sandan Musulunci ta jigar Kano, wacce aka fi sani da Hisbah ta kama mutumin da ake zargi da ajalin jaririyar ɗiyarsa kwana ɗaya bayan haihuwarta.
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da samun nasarar cafke wani gawurtaccen ɗan bindiga da ya addabi jama'a wanda ta daɗe tana nema a jihar.
Kotu ta tasa keyar wani matashi kan satar kodar wani dan jihar Benue ba tare da ya sani ba, tuni ya siyar da kodar a birnin Tarayya Abuja kan makudan kudade.
Wasu matasa a jihar Kaduna sun kai farmaki tare da rusa gida da kuma makarantar malamin da ke ikirarin halatta cin naman kare da dalibansa a jihar.
Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shahararren Fasto mai suna Usman Umaru da wasu mutane biyu a karamar hukumar Jos ta Gabas da ke jihar Plateau.
Dubun wani dan sanda, Yusuf Anas ya cika bayan ya bayyana kansa a matsayin jami'in rundunar da kuma tura sakon bogi na biyan kudin wata waya da ya siya a jihar Ondo.
Wani jami'in Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa, FRSC ya rasa ransa bayan direban babbar mota ya tunkudo shi kasa tare da murkushe shi har lahira a hanyar Abuja.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari