'Yan Sanda Sun Tsare Wani Matashi Kan Zargin Sheke Mahaifiyarsa Har Lahira, Ya Na Asibitin Kwakwalwa

'Yan Sanda Sun Tsare Wani Matashi Kan Zargin Sheke Mahaifiyarsa Har Lahira, Ya Na Asibitin Kwakwalwa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wani matashi da ake zargin ya shake wuyan mahaifiyarsa
  • Wanda ake zargin Sikiru Samson ya aikata hakan ne a kauyen Itanrin da ke karamar hukumar Ijebu-Ode a cikin jihar Ogun
  • Rundunar ta ce yanzu haka Sikiru ya na asibiti bangaren masu ciwon kwakwalwa don duba lafiyarsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Wani matashi mai suna Samson Sikiru ya shake wuyar Mahaifiyarsa har lahira a karamar hukumar Ijebu-Ode da ke jihar Ogun.

Matashin wanda ake zargin yana shan kwayoyin maye ya aikata hakan ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli a kauyen Itanrin.

Jami'an 'Yan Sanda Sun Tsare Matashi Kan Zargin Shake Mahaifiyarsa Har Lahira A Ogun
Rundunar 'Yan Sanda Ta Na Tsare Da Wani Matashi Kan Zargin Shake Mahaifiyarsa Har Lahira. Hoto: GistReel.
Asali: Facebook

Kanin wanda ake zargin shi ya tona asiri bayan ya dawo daga aiki ya tarar da mahaifiyar tasu ta mutu.

Yadda matashin ya shake wuyan mahaifyarsa

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

Vanguard ta tattaro cewa makwabta sun kama Samson tare da mika shi ga 'yan sanda bayan sun fahimci shi ya kashe mahaifiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, mai hulda da jama'a na rundunar a jihar, Omotola Odutola ta ce sun samu labarin kashe matar.

Ta ce yanzu haka Samson na asibiti a bangaren masu ciwon kwakwalwa don ba shi kulawa.

Ta kara da cewa a lokuta da dama 'yan uwan nasa suna daure shi don kada ya ji wa wani ciwo ko kansa, cewar Channels TV.

Ta ce:

"Ya na zuwa wurin mahaifiyarsa a lokutan bikin sallah, duk da dai ya na da matsala amma an tabbatar da cewa abin nashi na yin sauki.
"Sai dai ba a sani ba ko akwai wani abu tsakaninshi da mahaifiyar, amma a ranar an daure shi bayan ya kubuta ne sai ya haurarwa mahaifiyarsa."

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Masoyin Tinubu Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, Ya Yi Iƙirarin Daukar Mummunan Mataki

'Yan sanda suna tsare da matashin a asibiti don duba kwakwalwarsa

Omotola ta ce an samu ciwo a jikin matar alamun akwai saka karfi yayin artabun da suka yi da mahaifiyar tasa.

Ta kara da cewa:

"Sukiru ya na hannun jami'an 'yan sanda amma har yanzu ba a samu komai daga gare shi ba tun da ko amsa daya bai bayar ba daga tambayoyin da aka masa."

Yan Sanda Sun Cafke Wata Da Ta Kwarawa Ma’akaciyar Mijinta Ruwan Zafi Kan Zargin Badala

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta cafke wata mata da ta kwarawa ma'aikaciyar mijinta ruwan zafi.

Matar mai suna Esther ta na zargin Endurance da cewa suna nema da mijinta da sunan ita ma'aikaciyarsa ne.

Rundunar ta ce ta tsare Esther a komarta har sai ta kammala bincike za ta tura ta kotu don girban abin da ta shuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel