Musulmai
Sheikh Sheikh Sulaiman Faruq Onikijipa daga Kwara ya bukaci Olusegun Obasanjo ya karɓi Musulunci saboda irin gudummawar da ya bayar wajen gina masallatai.
Cif Olusegun Obasanjo da Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar sun bukaci 'yan Najeriya su rika ayyukan alheri domin samun lada daga Allah yayin shirin gyaran masallaci.
Malamin Musulunci a Kano, Sheikh Adam Abdallah Kano ya yi ruwan addu'o'i ga kungiyar ECOWAS da masu goyon bayanta kan dokar batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Makwanni da rasuwar Malam Idris Dutsen Tanshi, an bukaci duk wanda ya sayi fili daga marigayi ya hallara a filin a ranakun Asabar da Lahadi masu zuwa.
Yayin da take kokarin ba kowa hakkinsa, Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sanya Hijabi ga matan ma’aikatan tsaro domin basu damar bin addininsu.
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) a karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta yi fatali da hukuncin kotun ECOWAS.
Saudiyya ta saka 29 ga Afrilu a matsayin ranar ƙarshe da maniyyatan Umrah za su bar ƙasar. Wanda ya karya dokar zai fuskanci hukuncin tara da daurin watanni.
Wata kungiya mai rajin kare hakkin ɗan adam watau RID ta bukaci gwamnatin jihar Kano ta sauya dokokin ɓatanci sakamakon hukuncin da kotun koli ta yanke.
Shugaban Izala ta Najeriya, Dr. Abdullahi Bala Lau ya yi ta'aziyyar rasuwar shugaban Ahlus Sunnah na ƙasar Togo, Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu, ya masa addu'a.
Musulmai
Samu kari