Manyan Labarai A Yau
Tsohon gwamnan soji na Cross River da Delta a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha, Commodore Ibrahim Kefas (mai ritaya), ya rasu a ranar Juma’a, 1 Oktoba.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jawabinsa na yanci ya da umarnin daukar mataki a kan ’yan kasuwar da ke saye kayan abinci suna boyewa domin samun kazamar riba.
A yanzu Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin maido da ayyukan sadarwa a fadin garin Gusau, babban birnin jihar daga ranar yau Juma'a, 1 ga watan Oktoba.
Masu zanga-zanga sun mamaye gadar Dantata da ke kan shaharariyar hanyar filin jirgin sama a Abuja, suna neman shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi murabus.
Biyo bayan kiran shugaba Muhammadu Buhari na hadin kan kasa, yan Najeriya da dama sun shiga shafukan sada zumunta don maida martani kan kalamansa da zarginsa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakonsa na bikin ranar samun yanci, ya yi ikirarin cewa dan majalisar tarayya ne ke daukar nauyin masu tayar da tarzomar kasar.
Jami’an ‘yan sanda a kasar Saliyo sun cafke jagoran kungiyar IPOB, Chidi Uchendu, a wurin kasuwancinsa a yankin Freetown a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba.
Kwamishina yaɗa labaru na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Dosara, ya bayyana cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu a matakin datse hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dakta Usman Abubakar a matsayin sabon daraktan kiwon lafiya na cibiyar lafiya ta tarayya (FMC) Bida, Neja.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari