Da dumi-dumi: Tsohon gwamnan Najeriya ya mutu a ranar bikin samun 'yancin kai
- Commodore Ibrahim Kefas (mai ritaya), tsohon gwamnan Delta da Cross River a mulkin soja, ya rasu a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba
- Marigayi Kefas wanda ya rasu yana da shekara 73 ya yi aiki a matsayin jagora a mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha
- Kefas ya sha kaye a hannun dan takarar PDP, Danbaba Suntai, a jihar Taraba yayin zaben gwamna na 2007
A daidai lokacin da 'yan Najeriya suke bikin murnar ranar yancin kan kasarsu, sai ga wani labari mara dadi na wani mutuwa da ya zo a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba.
Kamar yadda AIT News ta ruwaito, tsohon gwamnan na Cross River da Delta a mulkin soji, Commodore Ibrahim Kefas (mai ritaya), ya rasu a ranar Juma'a a wani asibitin Abuja yana da shekaru 73.
An binne marigayin daidai da koyarwar addinin Islama a wannan ranar.
Marigayi Kefas ya yi gwamnan soja na jihohin biyu tsakanin 1993 zuwa 1996 a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha.
Shekaru bayan haka, Kefas ya tsaya takarar gwamnan Taraba a 2007 amma ya sha kaye a hannun dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Danbaba Suntai.
Tsohon gwamnan mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya rasu
A wani labarin, mun kawo cewa tsohon gwamnan jihohin Legas da Imo a zamanin mulkin soja, Rear Admiral Ndubisi Kanu (mai murabus) ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.
Abokiyar huldar Kanu kuma mukusanciyarsa, Mrs Joe Okei-Odumakin ta tabbatar wa The Punch labarin a ranar Laraba.
Kanu, wadda tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Murtala Mohammed ya nada cikin majalisar kolin sojoji a shekarar 1975, daga bisani ya zama mai rajin kare hakkin bil adama bayan barin aikin soja.
Asali: Legit.ng