Faransa za ta taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar rashin tsaro na yanki - Macron

Faransa za ta taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar rashin tsaro na yanki - Macron

  • Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya jadadda kudirinsa na zurfafa alakar diflomasiyya da Najeriya
  • Macron a sakon taya murnar ranar yancin kai zuwa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin tallafawa kasar wajen tunkarar matsalolin yanki da na tsaro
  • Ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya ne ya fitar da sanarwar a ranar Asabar, 2 ga watan Oktoba

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alkawarin zurfafa alakar diflomasiyya da Najeriya, musamman wajen tunkarar matsalolin yanki da na tsaro, Premium Times ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya ya fitar a ranar Asabar na sakon fatan alheri da Mista Macron ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari, don tunawa da bikin cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Read also

Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

Faransa za ta taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar rashin tsaro na yanki - Macron
Faransa za ta taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar rashin tsaro na yanki - Macron Hoto: The Sun
Source: UGC

Sanarwar ta nakalto Mista Macron ya sake jaddada kudurinsa na kashin kansa kan alakar da ke tsakanin Faransa da Najeriya wanda ke haifar da karfin tattalin arziki da yawan jama'a.

“Na yi imanin cewa yana da amfani ga kasashenmu biyu karfafa wannan alakar ta kowane bangare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tun lokacin da na kai ziyara a watan Yulin 2018, alakar da ke tsakanin kasashenmu ta ci gaba da karfafa, musamman a fannin tattalin arziki.
"Na yi farin cikin tarbanka a Paris a ranar 18 ga Mayu, a yayin da ka halarci Babban Taro kan Tallafin Tattalin Arzikin Afirka.
"Muna fatan kafa kungiyar kasuwanci na Franco-Nigerian, wacce ta hadu a watan Yunin da ya gabata a Fadar Versailles, za ta ba da damar samar da ayyuka da yawa tsakanin kamfanonin Faransa da na Najeriya."

Jaridar ta kuma ruwaito cewa Shugaba Macron ya yaba da karuwar adadin daliban Najeriya a Faransa don kara ba da gudummawa ga zurfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Read also

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

Ya kuma ba da tabbacin cewa kasashen biyu za su yi wasu abubuwa don cimma burin da ake bukata.

Ya ci gaba da cewa:

"Za mu iya yin ƙarin aiki tare, saboda Faransa da Najeriya suna da manufa iri ɗaya, a kan batutuwan yanki da na tsaro da kuma lamuran duniya.
"Don haka ina fatan kasashenmu za su zafafa mu'amalarsu kan dukkan wadannan batutuwa."

Ya yi fatan alheri ga Shugaba Buhari da 'yan Najeriya kan bikin zagayowar ranar samun 'yancin kai.

An kuma, wani mutum ya jefi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da ɗanyen ƙwai

A wani labari na daban, Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ji saukar kwai a kafadarsa bayan ya kai ziyara wani gidan cin abinci a kasar ta Faransa.

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, bayan jifar sa da kwai da wani ya yi, ya sauka a kafadar sa sannan ya fadi kasa ba tare da ya fashe a jikin sa ba.

Read also

Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu

Ya kai ziyara wani wurin cin abinci da Otal ne dake kudu maso gabashin birnin Lyon a ranar Litinin kamar yadda AFP ta ruwaito.

Source: Legit

Online view pixel