Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja

  • Gwamnatin Neja ta tabbatar da kisan sojojin Najeriya biyu a wani hari da ƴan bindiga suka kai yankin Kagara ta jihar
  • Gwamnna Abubakar Sani Bello ne ya tabbatar da haka yayin da ya ziyarci sojoji 12 da ke kwance a asibitin Ibrahim Badamasi Babangida a Minna
  • Ya kuma bayyana cewa an tafi da wasu sojojin zuwa Kaduna domin kula da lafiyarsu

Jihar Neja - Wani rahoton gidan talbijin na AIT ya kawo cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani hari da aka kai garin Kagara da fadar Sarkin, a jihar Neja.

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Minna, babbar birnin jihar, jim kadan bayan ya ziyarci sojoji goma sha biyu da suka jikkata wadanda ke karbar magani a asibitin Ibrahim Badamasi Babangida.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja
Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Gwamnan ya kuma ce wasu daga cikin sojojin da suka jikkata suna samun kulawar likitoci a wani asibiti da ke Kaduna, sashin Hausa na BBC ya kuma ruwaito.

Gwamnan a cikin wata sanarwa daga Babbar Sakatariyar Yada Labarai, Mary Berje, ya ce babu takamaiman adadin wadanda suka mutu.

Gwamnan ya nuna damuwarsa game da karuwar 'yan fashi da yadda suke tsarawa da aiwatar da hare-hare kan garuruwa.

Don haka ya umarci mutane da su kasance masu taka tsantsan game da tsaro tare da bayar da rahoton duk wani motsi da basu aminta da shi ba.

Gwamna Bello ya kuma nuna damuwa game da wasu garuruwa da ke dauke da 'yan fashi.

'Yan bindiga sun sace sakataren dindindin na Neja da jikarsa

Kara karanta wannan

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

A gefe guda, mun kawo cewa ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Dr. Ibrahim Garba Musa, babban sakatare a ma'aikatar sufuri ta Neja, a ranar Juma'a 1 ga watan Oktoba tare da jikarsa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan bindiga sun sace Musa ne a yankin Zugeru na jihar bayan bikin aure da ya halarta.

Labarin ya bayyana cewa 'yan bindiga sun shiga gidan sakataren na din-din-din ta hanyar fasa kofar gidan, Punch ta kuma ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel