Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun sace sakataren dindindin na Neja da jikarsa
- Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da babban sakataren din-din-din na ma'aikatar sufuri ta Neja da jikarsa
- Lamarin ya afku ne a gidansa na Zungeru a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba, inda ya je wani daurin aure
- Zuwa yanzu ba a ji ta bakin kakakin 'yan sandan jihar ba amma sakataren gwamnatin jihar ya ba da tabbacin ganin an ceto su cikin koshin lafiya
Jihar Neja - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Dr. Ibrahim Garba Musa, babban sakatare a ma'aikatar sufuri ta Neja, a ranar Juma'a 1 ga watan Oktoba tare da jikarsa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan bindiga sun sace Musa ne a yankin Zugeru na jihar bayan bikin aure da ya halarta.
Labarin ya bayyana cewa 'yan bindiga sun shiga gidan sakataren na din-din-din ta hanyar fasa kofar gidan, Punch ta kuma ruwaito.
Da yake magana kan lamarin, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya ce har yanzu bai tabbatar da lamarin ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai Matane ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta yi iya kokarin ta wajen ganin an ceto Musa lafiya.
Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Niger, DSP Abiodun Wasiu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
'Yan bindiga sun ƙona mutum 10 da ransu, sun yi wa wasu 15 yankan rago a Jihar Niger
A wnai labarin, wasu mutane da makamai da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kona mutane 10 da ransu a garin Kachiwe da ka mazabar Sarkin Pawa a karamar hukumar Munya na jihar Niger.
Yan bindigan sun kuma sace mutane bakwai yayin harin kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.
Rahoton na SaharaReporters ya ce sakataren karamar hukumar Munya na jihar, James Jagaba ya bada labarin abin da ya faru wanda ya kira 'mummunan lamari.'
Asali: Legit.ng