Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun saki babban hafsan soji mai ritaya, AVM Smith

Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun saki babban hafsan soji mai ritaya, AVM Smith

  • Rana ce ta farin ciki ga Air Vice Marshal (AVM) Sikiru Smith mai ritaya da iyalansa yayin da aka kubutar da shi daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi
  • An yi garkuwa da shugaban na NAF mai ritaya a wajen Legas a ranar Litinin, 27 ga Satumba, yayin da yake kula da aikin da ke gudana
  • Hakeem Odumosu, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas ne ya tabbatar da sakin Smith

Kwanaki biyar bayan sace shi a yankin Langbasa da ke Legas, ‘yan bindiga sun sako babban soja mai ritaya, AVM Sikiru Smith mai ritaya, jaridar The Nation ta ruwaito.

‘Yan sanda sun kubutar da Smith daga bakin ruwa a Langbasa inda masu garkuwa da mutanen suka yi watsi da shi da misalin karfe 4:00 na asuba a ranar Asabar, 2 ga watan Oktoba.

Read also

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun saki babban hafsan soji mai ritaya, AVM Smith
Masu garkuwa da mutane sun saki babban hafsan soji mai ritaya, AVM Smith Hoto: Premium Times
Source: UGC

An tattaro cewa wasu 'yan bindiga da suka yi garkuwa da tsohon Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya (NAF) sun yi awon gaba da shi a cikin jirgin kwale-kwale zuwa inda ba a sani ba.

Don tabbatar da kubutar da shi lafiya, Sufeto Janar na 'yan sanda IGP Alkali Usman ya tura jami’an 'yan sanda na ruwa da runduna ta musamman daga Abuja don taimakawa rundunar ta Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake tabbatar da sakin nasa, Kwamishinan ‘yan sandan Legas, Hakeem Odumosu ya ce Smith ya koma ga iyalansa, ya kara da cewa har yanzu ana kokarin cafke masu garkuwa da mutanen.

Ya ce jami'an tsaro sun bi sahun masu laifin amma sun fi damuwa da dawowar sa lafiya.

Ya ce:

“Akwai wasu bayanai da ba zan iya ba ku ba amma ina tabbatar da cewa an kubutar da shi kuma ya koma ga danginsa.

Read also

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

“An fara aikin ne da misalin karfe 2:00 na tsakar dare, a karshe aka sauke shi a bakin ruwa na Langbasa da misalin karfe 4:00 na safe tare da wasu mutane.
"Za mu tabbatar da ganin cewa an tattara duk wadanda suka aikata laifin."

Rundunar 'yan sandan jihar ba ta iya tabbatar da ko an biya kudi don sakinsa ba, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas

A baya mun kawo cewa wasu yan bindiga sun yi awon gaba da Air Vice Marshal Sikiru Smith (retd.), a unguwar Ajah dake jihar Legas, rahoton Punch.

Wanda aka sace tsohon babban Soja ne kuma dan'uwa ga shugaban hukumar jin dadin yan sanda, Musuliu Smith.

An tattaro cewa yan bindigan sun saceshi ne yayinda yake wajen duba aikin da kamfaninsa Double Wealth Ventures Limited ke yi a Ajah.

Read also

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

Source: Legit.ng

Online view pixel