Manyan Labarai A Yau
Wata baƙuwar cuta wacce ba a san musabbabinta ba, ta ɓulla a garin Kafanchan na jihar Kaduna. Cutar ta janyo kulle makarantu yayin da mutum huɗu suka rasu.
Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadin Kai' sun ragargaji ƴan ta'adda a jihar Borno. Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda shida tare da ƙwato makamai.
Masu goyon bayan Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan cire tallafin man fetur, sun gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya da ke a birnin tarayya Abuja.
Batun cewa mai shari'a Ugo na kotun ɗaukaka ƙara ya yi murabus da fitar da sanarwa cewa an buƙace shi ya yi wa wani ɗan takara sauƙi, ƙarya ce tsagwaronta.
Kakakin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu, Bayo Ananuga ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur yana nan tafe.
Kamfanin simintin Aliko Dangote ya gudanar da shirin sake siyan hannun jari daga masu zuba hannun jari a kamfanin. Kamfanin ya siya hannun jari 168m a shirin.
Shaidan da jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Isah Muhammad Ashiru Kudan, suka gabatar a gaban kotun zaɓe ya kiɗime inda ya yi magana daga baya ya zo ya warwareta.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da mataimakinsa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da wasu gwamnonin APC a Villa.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi namijin ƙoƙari a jihar Zamfara, inda suka ceto mutane masu yawa da miyagun ƴan bindiga suka yi garƙuwa da su a wani artabu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari