Gagarumin Sauyi: Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Tsige Firayim Minista, Ya Rusa Gwamnati

Gagarumin Sauyi: Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Tsige Firayim Minista, Ya Rusa Gwamnati

  • Shugaban kasar Ivory Coast ya tsige Firayim Ministakasar, Patrick Achi daga kan kujerarsa a ranar Juma'a, 6 ga watan Okotoba
  • Shugaba Alassane Ouattara ya tsige Firayim Ministan sanan ya sanar da shirin kafa sabuwar gwamnati
  • Ouattara ya yanke wannan shawarar ne shekaru biyu kafin zaben shugaban kasa mai zuwa a Ivory Coast

Côte d'Ivoire, Yamoussoukro - Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya tsige Firayim Ministansa, Patrick Achi, a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba.

Shugaban kasar Ivory Coast ya tsige firaministansa
Gagarumin Sauyi: Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Tsige Firaminista, Ya Rusa Gwamnati Hoto: @AOuattara_PRCI
Asali: Twitter

Reuters ta rahoto cewa Ouattara ya tsige Firayim Ministansa sannan ya sanar da shirin kafa sabuwar gwamnati, shekaru biyu kafin zaben shugaban kasar mai zuwa.

Bloomberg ta rahoto cewa Ouattara ya sanya hannu a wata doka "kawo karshen ayyukan Firayim Ministan, wanda shine shugaban gwamnati, da na mambobin gwamnati", a cewar wata sanarwa da babban sakataren shugaban kasa Abdourahmane Cisse ya karanta.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Fadi Yadda Buhari Ya Durkusar da Kasuwancinsa Wajen Fallasa Tinubu

Ko da dai ba a bayar da dalilin daukar matakin na ba zato ba tsammani ba, amma jam'iyya mai mulki ta lashe mafi yawan kujeru a zaben kananan hukumomi a watan jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, shugaban kasar ya nuna "godiyarsa ga Firayim Minista Patrick Achi da daukacin mambobin gwamnatin kan hidimtawa kasar da suka yi tsawon shekarun da suka gabata."

A halin da ake ciki, Ivory Coast za ta gudanar da zaben shugaban kasa a 2025. Ouattara, wanda zarce a 2020, bai bayyana ko zai sake tsayawa takara ba.

Tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Konan Bedie, ya rasu yana da shekaru 89

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa tsohon shugaban ƙasar Ivory Coast, Henri Konan Bedie, wanda ya mamaye siyasar ƙasar da ke yammacin nahiyar Afirka na tsawon lokaci, ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Takardun Tinubu: Atiku Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Ya Ke Yaki Da Bola, Ya Nemi Goyon Baya

Wani ɗan uwansa na kusa-kusa ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar ya mutu yana da shekaru 89 a duniya ranar Talata, 1 ga watan Agusta, 2023.

Marigayi Bedie ya riƙe kujerar shugaban kasar Ivory Coast tun daga shekarar 1993 har zuwa lokacin da aka fatattake shi a shekarar 1999.

Lokacin yana ɗan shekara 86 a duniya, Konan Bedie ya sake neman zama shugaban ƙasa amma ya sha kaye a hannun babban abokin adawarsa na siyasa, shugaba Alassane Ouattara a zaɓen 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel