Manyan Labarai A Yau
Gwamnonin APC na Kudu maso Yamma, Sanwo-Olu (Legas), Biodun Oyebanji (Ekiti) da Dapo Abiodun (Ogun) sun ziyarci gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a ofishinsa.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Enugu, ta bayar da umarnin a maye gurbin Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya yi magana kan muhimmancin bin doka da oda da barazanar da ƙin yin hakan ka iya yi ga dimokuradiyya.
Wata mata yar Najeriya ta yi bidiyo mai ban dariya na yawon neman gida a UK. Ta bayyana gaskiyar abun da ke zuciyarta game da gidan da dalilinta na kin karbar gidan.
Shugaban shiyya na jam’iyyar SDP a Kogi, Sunday Atabo ya na kwance a asibiti. Jam’iyyar adawar ta yi kira ga jami’an tsaro su yi bincike a kan aika-aikar da aka yi.
Wata mata a jihar Anambra ta sanya jikanta a kasuwa inda ta karɓi kuɗinsa ba tare da sanin mahaifiyarsa ba. Matar dai ta cefanar da jaririn ne kan kuɗi N50,000.
Olanipekun Olukoyede ya fara mulki da matsala, ana yi wa kujerarsa barazana. Tun kafin ya gyara zama a ofis, an shigar da kara a kotu za a tunbuke shugaban na EFCC.
Kotun ƙoli ta ɗage sauraron ɗaukaka ƙarar da Atiku Abubakar, Peter Obi suka shigar suna ƙalubalantar nasarar shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2023.
Kotun ƙoli a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoban 2023, yayin da take sauraron ɗaukaka ƙarar da Atiku, PDP suka yi, ta ce akwai wasiƙu masu ruɗani daga jami'ar CSU.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari