Ranar Sakamako: Nuhu Ribadu, Gbajabiamila Sun Gana Da Lauyan Atiku a Kotun Koli

Ranar Sakamako: Nuhu Ribadu, Gbajabiamila Sun Gana Da Lauyan Atiku a Kotun Koli

  • Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben shugaban kasa nna 2023 a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, watanni bayan gudanar da zaben
  • Yayin da INEC ta ayyana Bola Ahmed Tinubu, jigon jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, abokan hamayyarsa sun kalubalanci nasarar a kotu
  • A ranar hukuncin karshe da kotun koli za ta yanke, manyan yan siyasar da wakilan gwamnati sun hallara don shaida yadda zaman zai kaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da babban mai ba kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu sun gana da lauyan Atiku Abubakar, Chris Uche (SAN) a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

An gano su suna gaggaisawa yayin da suke jiran kotun koli ta zartar da hukunci kan zaben Shugaban kasa Tinubu wanda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana nasararsa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Ribadu da Gbajabiamila sun gana da lauyan Atiku
Ranar Sakamako: Nuhu Ribadu, Gbajabiamila Sun Gana Da Lauyan Atiku a Kotun Koli Hoto: @akibu_adebayo
Asali: Twitter

Kotun koli: Yan adawar siyasa sun hadu sun gaisa

Manyan jam'iyyun adawar Najeriya sun shigar da kara bayan an ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar a watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu mai shekaru 71 shine dan takarar jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'u kusan miliyan 8.8 - kimanin kaso 36.6 na jimlar kuri'un, kamar yadda shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana.

Ya kayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku na PDP da dan takara na uku, Peter Obi, wanda shine zabin matasa da dama da jam'iyyarsa ta LP.

Abubuwan da kotun koli za ta duba

Kotun koli dai ta tsayar da ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba domin yanke hukunci kan ƙararraki biyu da aka ɗaukaka da ke neman soke zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Alkalin Alkalai Ariwoola Ya Amince a Haska Hukuncin Kotun Koli Kai Tsaye

Idan dai ba a manta ba a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba ne kotun koli ta fara sauraron ƙararrakin da ƴan takarar jam'iyyun adawa suka shigar na soke hukuncin kotun zaɓe da ke tabbatar da nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen watan Fabrairu.

Ƴan takarar da ke ƙalubalantar zaɓen dai su ne Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel