Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7 a Wani Kazamin Hari a Jihar Benue

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7 a Wani Kazamin Hari a Jihar Benue

  • Wasu miyagun mahara ɗauke da makamai sun aikata aikin ta'addanci a wasu ƙauyuka guda biyu na jihar Benue
  • Maharan waɗanɗa aka kyautata zaton ƴan bindiga ne sun halaka mutum baƙwai a ƙauyen Tse Gamber da wani ƙauye a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma
  • Jam'ar hulɗa da jama'a ta ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin, sai dai ta ce mutum uku ne kawai suka halaka

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu mahara ɗauke da makamai sun halaka mutane bakwai a wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue.

Mazauna yankin sun ce an kai hare-haren ne a ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba, a ƙauyen Tse Gamber da kuma wani ƙauye kusa da Naka-Agagbe, duk a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun halaka babban limami a jihar Borno

Yan bindiga sun halaka mutum 7 a Benue
Yan bindiga sun halaka mutum 7 a kauyukan Benue Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mazauna ƙauyen sun yi bayani

Mazauna kauyen sun ce yayin da aka kashe mutum huɗu a harin da aka kai da sanyin safiyar Lahadi a Tse Gamber da ke gundumar Sengev, an kashe mutum uku da yammacin wannan rana a sansanin Nagi da ke gundumar Mbachohon, wanda da ke kan hanyar Naka-Agagbe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Terna Ibaah Jacob, jami'i mai kula da sansanin ƴan gudun hijira a Agagbe, ya ce wasu daga cikin waɗanda suka mutun an raba su ne daga ƙauyukansu kuma suna zaune ne a sansanonin ƴan gudun hijira.

Jacob ya yi nuni da cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka halakan, Gamber Awuhe, mai shekara 45, an kashe shi ne a yammacin Lahadi, lokacin da ya je kamun kifi, hanyar da kawai yake amfani da ita wajen ciyar da iyalinsa.

Menene martanin da ƴan sanda suka yi?

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Solomon Dalung Ya Bayyana Mafita 1 Kan Rikice-Rikicen Jihar Plateau

Jami'ar hulɗa da jama'a ta ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene ta tabbatar da mutuwar mutum uku.

"Wannan ƙauyen mu ne (Tse Gamber). An halaka uku daga cikin ƴan uwa na, wannan shi ne adadin mutanen." A cewarta.

'Yan Bindiga Sun Halaka Tsohon Shugaban Karamar Hukuma

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka wani tsohon shugaban ƙaramar hukuma a jihar Benue, bayan sun yi kwanaki da sace shi.

Marigayin mai suna Washima Erukaa wani dattijo ne da ya taba zama shugaban karamar hukumar Katsina Ala da Ukum a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel