"Lokacin Mu Ne a Kogi": Yadda Ƙabilu 3 Ke Neman Ɗarewa Kan Mulkin Jihar Kogi

"Lokacin Mu Ne a Kogi": Yadda Ƙabilu 3 Ke Neman Ɗarewa Kan Mulkin Jihar Kogi

  • Ɗan jarida Arogbonlo Israel yayi nazari akan yadda ɓabilanci zai taka rawar gani a zaɓen gwamnan Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba
  • Manyan ƙabilu uku - Okun, Ebira, da Igala na da ƴan takara da za su fafata a zaɓen gwamnan na ranar Asabar
  • Israel ya buƙaci masu kaɗa kuri’a da su ba da fifiko wajen zaɓen ƴan takarar da suka cancanta ba ƙabilanci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lokoja, jiihar Kogi - A yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar Kogi, Arogbonlo Israel, ɗan jarida kuma mai fafutukar neman zaman lafiya, ya yi nazari kan al'amuran siyasar jihar Kogi.

Israel ya yi nuni da cewa, a dai-dai lokacin da ake sa ran zaɓen gwamnan Kogi, an fi mayar da hankali kan batun ‘awa lo kan’ wanda ke nufin 'lokacin mu ne', wani ra’ayin ƙabilanci da ke tasiri a yanayin siyasa.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamnan jihar Kogi: Ƴan Najeriya sun yi hasashen wanda zai yi nasara

Kabilu da ke neman samar da gwamnan Kogi
Manyan kabilu uku na neman samar da gwamnan Kogi Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo/Murtala Yakubu Ajaka/Dino Melaye
Asali: Facebook

Duk da wadatar albarkatu, Kogi na fama da ƙalubale masu yawa, waɗanda aka danganta da matsalolin shugabanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karanta nazarinsa a ƙasa:

Kogi 2023 da batun ‘awa lo kan’

Kogi, wacce ta shahara wajen wayar da kan jama'a, jiha ce da ke alfahari da kanta a matsayin cibiyar jan hankali ta fuskar siyasar Najeriya a yau.

Jihar Kogi da ke da iyaka da jihohi 10, ta kasance a tsakiyar Najeriya, inda ta yi iyakoki da jihohin Kudancin Najeriya da na Arewacin Najeriya.

To amma abin tambaya a nan shi ne, me ya sa har yanzu Kogi ke fuskantar ƙalubale a yau duk da albarkatun da take da su? Amsa mai sauƙi ita ce - jagoranci.

Idan muka yi la’akari da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, zaɓen ya fi zafi ne a tsakanin ƴan takara uku waɗanda suka fito daga shiyyoyin siyasa uku na jihar.

Kara karanta wannan

To Fa: Ana jajibirin zaɓe, Ɗan takarar Gwamna na jam'iyyar APC ya sha da ƙyar, bayanai sun fito

Manyan ƴan takara uku sun haɗa da:

  • Dino Melaye na jam'iyyar PDP - Okun
  • Usman Ododo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) - Ebira
  • Murtala Ajaka na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) - Igala

Waɗannan ƴan takara guda uku ta tsarin lissafi sun raba masu zaɓe bisa ra'ayin ƙabilanci, wanda kuma hakan zai taka rawar gani kan yadda zaɓen zai kaya.

Zaɓen gwamnan Kogi 2023: Ajandar Okun

Kamar yadda aka riƙa batun ‘Yoruba lo kan’ a lokacin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023, al’ummar Okun (Kogi ta Yamma) sun yi imanin cewa lokaci ne na yankin na samar da gwamna idan aka bi tsarin karɓa-karɓa na shiyya-shiyya.

Tun daga 1999, Okun sun kasance saniyar ware ta fuskar shugabanci a jihar, inda wasu ƴan siyasar yankin sun taka rawar gani wajen kawo wa yankin cikas. Wannan ba shakka, zai taka rawar gani kan yadda masu kaɗa ƙuri'a za su yi zaɓe a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

"Ina kwance a asibiti na kusa mutuwa": Jigon APC mara lafiya ya koka

Zaɓen Gwamnan Kogi 2023: Ajandar Ebira

Kamar takwarorinsu na Okun, su ma Ebira ba a keɓe su daga nuna ra'ayin ba don siyar da ɗan takarar da wasu masu sukar siyasa ke kallonsa a matsayin "mara farin jini".

Ahmed Usman Ododo yana ƙoƙarin yin amfani da farin jinin Gwamna Yahaya Bello, wanda ya ke cigaba da yi masa yaƙin neman zaɓe duk da adawar da yake fuskanta.

Shin shirin Ebira zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance yadda Ebira za su yi zaɓe? Ba za a samu amsar wannan tambayar ba har sai bayan zaɓe.

Zaɓen gwamnan Kogi 2023: Ajandar gala

Ajandaer Igala ta kutsa kai cikin siyasar Kogi a ƴan kwanakin nan biyo bayan fitowar Muritala Ajaka a matsayin ɗan takarar jam’iyyar SDP.

Hakan ya sanya ɗan takarar ya samu goyon baya sosai daga yankin wanda zai taka muhimmiyar rawa a zaɓen na ranar Asabar.

Duk da sun mulki jihar na tsawon shekaru 16, Igala sun yi amanna cewa kamata ya yi mulki ya koma yankin bayan shekaru takwas na gwamnatin Yahaya Bello. Zaɓen ranar 11 ga Nuwamba zai yanke hukunci idan hakan zai zama gaskiya ko kuma ya cigaba da zama a matsayin mafarki.

Kara karanta wannan

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta caccaki hukuncin kotun koli da nasarar Tinubu

Zaɓen gwamnan Kogi 2023: Wanene ya kamata ya yi nasara?

Abin da Kogi ke buƙata a yanzu ba wai shugaba mai kabilanci ba ne, suna buƙatar shugaba ne wanda zai wakilci kowa ba tare da la’akari da ƙabilanci ko addini ba.

Yanzu dai ya rage ga masu jefa ƙuri'a a ranar Asabar, wajen yin zaɓen da ya dace na ɗan takarar da zai ciyar da jihar gaba.

Zaɓen Kogi: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara

A wani labarin kuma, fitaccen malamin addini, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi.

Babban faston ya yi hasashen cewa ɗan takarar jam'iyyar APC, Ahmed Usman Ododo zai lashe zaɓen gwamnan na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel