Manyan Labarai A Yau
Wata kotun majistare mai zama a birnin Port Harcourt na jihar Rivers, ta tura wasu mutum biyu zuwa gidan gyaran hali bisa cin zarafin wani tsohon kan satar mazakuta.
Wata mata yar shekaru 30 da ta auri mahaifin kawarta mai shekaru 87 ta magantu kan yadda suka fada tarkon son junansu a ranar farko da suka hadu. Suna da yara biyu.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa za a iya magance matsalar tsaro ne a yankin Arewa maso Gabas idan masu ruwa da tsaki sun haɗa kai.
An ba gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akinkunrin Akeredolu, wa'adin sa'o'i 72 domin ya miƙa mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa saboda rashin lafiyarsa.
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya yi magana kan sake zaɓen Gwamna Duoye Diri a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Alkalin babban kotun tarayya da ke Abuja ya bada umurnin a tsare Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Yan Najeriya sun fito dandalin soshiyal midiya inda suka tofa albarkacin bakunansu a kan hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige Abba gida-gida daga gwamna.
Yan Najeriya a soshiyal midiya sun caccaki zababben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo kan durkusawa a gaban Gwamna Yahaya Bello don gabatar masa da satifiket dinsa.
Wata mata wacce ke dauke da dabbare-dabbaren baki a fuskarta ta yadu bayan ta ba da labarin abun da ya haddasa mata haka. Jama’a sun tausaya mata a sashin sharhi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari