Tashin Hankali Yayin da Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Jihar Kano, Mutane da Dama Sun Jikkata

Tashin Hankali Yayin da Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Jihar Kano, Mutane da Dama Sun Jikkata

  • An samu tashin hankali bayan wasu makiyaya sun far wa mutane suna tsaka da aiki a gonakinsu a jihar Kano
  • Rikicin wanda ya auku a wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Dambatta ya jawo mutane da dama sun samu raunuka
  • Mutanen yankin sun buƙaci gwamnati da ta kawo musu ɗauki wajen shawo kan matsalar kafin abubuwa su taɓarɓare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mutane masu yawa sun jikkata bayan ɓarkewar wani rikici a tsakanin manoma da makiyaya a jihar Kano.

Rikicin dai ya ɓarke ne a ƙauyukan Dusai da Ƴan Gamji da ke a cikin ƙaramar hukumar Dambatta ta jihar, cewar rahoton Aminiya.

Rikicin manoma da makiyaya ya barke a Kano
An samu barkewar rikicin makiyaya da manoma a Kano Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya auku ne ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, lokacin da wasu makiyaya suka farmaki manoma da ke aiki a gonakinsu.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun halaka babban malamin addinin da suka sace bayan karɓar kuɗin fansa a Kogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin ya auku

Makiyayan dai sun harbi manoman da kibiyoyi tare da sarar su da adda bayan sun same su suna tsaka da aiki a gonakinsu.

Baffa Dambatta, wani mazaunin garin ya bayyana cewa wasu makiyaya sun ɗauki makamai sun far wa wasu manoma a lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu, wanda hakan ya jawo aka bar mutane kwance jina-jina.

Wani da ƴaƴansa biyu suka jikkata a rikicin ya bayyana cewa yana gida aka kira shi aka sanar da shi cewa makiyaya sun far wa ƴaƴansa, inda yana zuwa ya tarar da su cikin jini da kibiya a soke a jikinsu.

Dagacin garin Ƴan Gamji, Malam Yusha’u Galadima ya bayyana cewa mai unguwar Dusai ya kira ƴan sanda lokacin da rikicin ya ɓarke, amma ba su kawo ɗauki a kan lokaci ba.

Kara karanta wannan

Yajin NLC: Harkoki sun tsaya cak yayin da ma'aikata suka zaɓa wa kansu mafita a babban birnin jihar PDP

Mazauna garuruwan dai sun yi kira ga gwamnati da ta yi duk mai yiwuwa domin magance matsalar kafin abubuwa su lalace.

Al'amura sun daidaita inda mutanen garuruwan suka koma bakin aikinsu.

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, kan lamarin, amma bai dawo da saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Mutane da Dama Sun Mutu a Rikicin Manoma da Makiyaya

A wani labarin kuma, an samu asarar rayuka da dama a wani rikicin manoma da makiyaya da ya ɓarƙe a jihar Kogi.

Rikicin dai ya fara ne bayan wasu mahara sun mamayi manomi ɗaya a hanyarsa ta zuwa gona, inda suka halaka shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel