Manyan Labarai A Yau
Wani kamfanin sufuri na Najeriya, mai suna Egora Technology ya kaddamar da adaidaita sahu samu mai aiki da man fetur da iskar gas duk a lokaci guda.
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta samu nasarar halaka yan bindiga shida da suka addabi wani yanki a jihar. Rundunar ta kuma kwato kayayyaki masu yawa a wajensu.
Diyar Marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu, Ololade ta haddasa yar dirama yayin da ta bukaci yan jarida da su bar gidan mahaifinta, ta fadi dalilinta na yin haka.
Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) da takwararta ta NEN sun ankarar da gwamnayin tarayya kam shirin da ake yi na kawo hargitsi a yankin Arewacin Najeriya.
Yan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Taraba bayan sun dira a wata babbar kasuwa lokacin da ake tsaka da gudanar da harkokin kasuwanci. Sun sace mutane da dama.
Fasto Osagie Ize-Iyamu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2024.
An shiga jimami a jihar Imo bayan wata budurwa ta yi ajalin saurayinta ɗan sanda har lahira. Budurwar dai ta bindige ɗan sandan ne har lahira da bindigarsa.
Gwamnatin jihar Zamfara ta kulle wasu kasuwannin shanu 11 a fadin jihar bayan ta gano miyagun yan bindiga na gudanar da hada-hadar kasuwanci a cikinsu.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'Abba, wanda ya rasu a Abuja.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari