Shugaba Tinubu Ya Ba Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega Sabon Mukami

Shugaba Tinubu Ya Ba Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega Sabon Mukami

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tuna da tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a rabon muƙaman da yake yi
  • Shugaba Tinubu ya naɗa Farfesa Attahiru Jega muƙamin shugaban kwamitin gyara kan harkokin kiwon dabbobi
  • Tinubu ya sanar da naɗin da ya yiwa Jega ne a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin a fadar shugaban ƙasa ranar Talata, 9 ga watan Yulin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega muƙami.

An bayyana naɗin ne a ranar Talata lokacin da Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin aiwatar da garambawul kan harkokin kiwon dabbobi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisa ta jawo hankalin Tinubu kan yunwa a kasa, ta ba shi mafita

Shugaba Tinubu ya ba Jega mukami
Shugaba Tinubu ya nada Attahiru Jega sabon mukami Hoto: Stringer
Asali: Getty Images

Tinubu ya naɗa Attahiru Jega sabon muƙami

An naɗa Attahiru Jega a matsayin shugaban kwamitin wanda aka kafa domin magance matsalolin da ke kawo cikas ga aikin noma a ƙasar nan, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa aiwatar da gyararrakin na buƙatar haɗin kan dukkanin mambobin kwamitin waɗanda aka zaɓo daga ɓangarori daban-daban, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

"Daga nan zan yi kira ga kowa da kowa da ya cire batun siyasa a nan. Zan zama shugaban kwamitin a matsayin shugaban ƙasa sannan na naɗa Farfesa Attahiru Jega a matsayin mataimakina ko shugaba."
"Wannan ba batun siyasa bane, wannan batun dama ne. Wannan batun al'ummarmu ne. Yayin da ba na nan, Jega zai yi shugabanci kuma ya ci gaba da inganta manufofinmu."

- Bola Tinubu

Shugaban ƙasan ya yi nuni da cewa hanyar kiwon dabbobi da ake da ita ta gargajiya na buƙatar a sake duba ta domin yi mata kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Shugabancin ECOWAS: Amfanin da Najeriya za ta samu sakamakon sake zaben Tinubu

Ya nuna cewa hakan zai yiwu ne tare da goyon bayan masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnonin jihohi domin samun sababbin damarmaki na ci gaba.

Majalisa ta shawarci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta buƙaci shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta magance matsalar ƙarancin abinci a faɗin ƙasar nan.

Hakan na zuwa ne biyo bayan ƙudirin da Sunday Karimi (APC, Kogi ta Yamma) ya gabatar kuma Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu) ya marawa baya a zauren majalisar ranar Talata, 9 ga watan Yulin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng