Manyan Labarai A Yau
Shugaban hukumar NYSC ya yi nuni da cewa matasa masu yiwa kasa hidima za su amfana da sabon mafi karancin albashi. Ya nuna cewa za a yi musu karin alawus.
Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta ce jami'anta sun samu nasarar hallaka wani mai garkuwa da mutane a jihar. 'Yan sandan sun kuma cafke takwarorinsa guda uku.
Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta kada kuri'ar amincewa da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani. An kada kuri'ar ne a wajen taro wanda El-Rufai ya ki halarta.
Darajar Naira ta farfado a kasuwa bayan kwashe kwanaki uku tana faduwa a kasuwa. A ranar 5 ga watan Yuli, darajar Naira ta kasu a kasuwannin 'yan canji.
Gwamnatin jihar Jigawa za ta ba manoma mutum 30,000 tallafi domin bunkasa harkokin noma a jihar. An ware manoman da za su amfana da shirin tallafin.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno. Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun kai farmaki a maboyar 'yan ta'addan.
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar hutu domin shigowa sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH. Gwamnatin ta ce babu aiki a ranar Litinin, 8 ga watan Yulin 2024.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa abin kunya ne a ce kasar nan har yanzu tana samar da 4.5GW ne kawai na wutar lantarki duk girmanta.
Jam'iyyar Labour a Ingila ta yi nasarar samun kujeru mafi rinjaye a zaben 'yan majalisa da aka yi a Ingila. Keir Starmer ne ya bayyana a sabon firayim minista.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari