Manyan Labarai A Yau
Matatar mai ta Dangote ta shirya fara sayar da man fetur a kasuwa. Matatar da gwamnati na tsara yadda za a rika jigila tare da sayar da man fetur din a kasuwa.
'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai mummunan hari a jihar Yobe. Miyagun masu dauke da makamai sun hallaka mutane masu yawa tare da kona shaguna.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta fito ta yi magana kan ikirarin da 'yan bindiga suka yi na kwace motoci masu sulke na dakarun sojojin Najeriya a jihar Zamfara.
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta lashe zaben shugabannin kananan hukumpmin da aka gudanar a jihar. APC ta cinye dukkanin kujerun hada na Kansiloli.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karbi jiga jigan jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar hallaka wani kasurgumin shugabammn 'yan ta'adda a jihar Kaduna. Sojojin sun sheke mayaka biyar.
Wani jirgin kwale kwale mai dauke da fasinjoji a jihar Bauchi ya kife a cikin tsakiyar kogi. An samu nasarar ceto mutum bakwai yayin da aka nemi sauran aka rasa.
Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, ya nuna kwarin gwiwarsa kan cewa nan ba ɗa jimawa ba za a shawo kan rikicin jam'iygar PDP. Ya ce suna kokari hakan.
Ambaliyar ruwa ta shafi mutane masu yawa a jihar Zamfara. Sama da mutum 10,000 ne suka rasa matsugunansu. Gwamnan jihar ya yi jajen aukuwar hakan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari