Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Yobe ta fito ta bayyana matsayarta kan batun fara biyan sabon mafi karancin albashin ma'aikata. Ta musanta cewa ta amince a fara biya.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar dakile yunkurin da 'yan bindiga suka yi na sace wata yarinya a jihar. Sun raunats 'yan bindigan.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa sunnshirya tsaf domin mayar da sauran jihohin da ke hannun 'yan adawa su dawo na APC.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Joe Ajaero, ya isa harabar ofishin 'yan sanda domin amsa gayyatar da aka yi masa kan zargin daukar nauyin ta'addanci.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhini kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka samu sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a johohi masu yawa na kasar nan.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga a jihar Kaduna. Sojojin sun kuma cafke wani daga cikin mai ba 'yan bindigan bayanai.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yiwa jigon PDP Bode George martani kan shawarar da ya ba shi ta ya hakura da yin takara a 2027.
Hukumar da ke kula da ƴan Najeriya mazauna kasahen waje ta gano bayanan matar da aka ji a bidiyo tana barazanar ƙarar da yarbawa mazauna ƙasar Kanada.
An gudanar da jana'izar da sojan ruwan Najeriya, Laftanal Kwamanda Gideon Yashim Gwaza, wanda ya rasu yayin ceto wasu mutane da jirginsu ya kusa nutsewa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari