'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Hallaka Mutane Masu Yawa a Wani Hare

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Hallaka Mutane Masu Yawa a Wani Hare

  • Ƴan ta'adɗan Boko Haram sun kai sabon harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka mutane da dama tare da ƙona shaguna da gidaje a harin wanda suka suka kai ranar Lahadi, 1 ga watan Satumban 2024
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Yobe wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce har yanzu ba a san adadin mutanen da suka rasu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Wasu ƴan ta'adda da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai hari a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Tofa: Ƴan sanda sun bayyana Bature da ya nemi kifar da gwamnatin Tinubu a Najeriya

Ƴan ta'addan sun hallaka mutane masu yawa waɗanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Yobe
'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka mutane a Yobe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A yayin harin, ƴan ta'addan sun kuma kwashe kayayyaki tare da ƙona shaguna da gidaje a ƙauyen, cewar rahoton jaridar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan ta'addan suka kai harin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a birnin Damaturu babban jihar Yobe, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Har yanzu ba mu tabbatar da adadin rayukan da aka rasa a harin wanda ya faru da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ranar Lahadi ba."
"Babagana Goni da Bako Ibrahim, mazauna ƙauyen Mafa ne suka kai rahoton lamarin ga ofishin ƴan sanda na Tarmuwa."
"Wasu ƴan ta’adda da ake zargin ƴan Boko Haram ne ɗauke da bindigu da RPG sun kai hari a ƙauyen Mafa a kan babura sama da 50 inda suka ƙona shaguna da gidaje da dama."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka kasurgumin shugaban 'yan ta'adda a Arewacin Najeriya

"Ƴan ta’addan sun kuma kashe mutane da dama, amma har yanzu ba mu san ainihin adadin waɗanda suka mutu ba."

- Dungus Abdulkarim

Kakakin ƴan sandan ya kuma ƙara da cewa ƴan ta'addan sun ajiye wasu takardu masu ɗauke da rubutun larabci.

Gwamnati ta shirya murƙushe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya umurci babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, tare da wasu hafsoshin tsaro da su koma jihar Sokoto.

Bisa wannan umarnin, shugabannin sojojin za su kula da hare-haren sojoji kan ƴan ta'addan daga Sokoto, da nufin daƙilewa da kuma kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng