Manyan Labarai A Yau
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a karamar hukumar Ibadanya jihar Oyo. Hatsarin wanda ya auku da safiyar ranar Litinin ya salwantar da rayukan mutum hudu.
Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana amfanin da ke tattare da cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar nan ta yi.
Wasu daga cikin mambobin jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP. Ficewarsu daga APC na zuwa ne ana dab da fara zaben ciyamomi.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya hakura da sake tsayawa takara a zabeɓ 2027.
Gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP za su gudanar da taro domin warware rikicin jam'iyyar. PDP dai na fama da rikice rikice masu yawa.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ja kunnen Sanata Ali Ndume kan sukar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. APC ta ce kamata ya yi ya ba shi shawara a kebe.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana yadda hatsarin motan da ya ritsa da dan tsohon gwamnan jihar Kaduna. Faisal Ahmed ya rasu ne a ranar Asabar.
Dan majalisar wakilai daga jihar Oyo, Aderemi Oseni, ya bukaci 'yan Najeriya su kara kai zuciya nesa kan gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kungiyar PAPSD kuma jagora a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Dakta Sani Shinkafi ya yabawa karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari