Tsadar Rayuwa: Dan Majalisa Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yi Wa Tinubu

Tsadar Rayuwa: Dan Majalisa Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yi Wa Tinubu

  • Wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Oyo ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Aderemi Oseni ya buƙaci a ƙarawa Shugaba Tinubu lokaci domin ya shawo kan matsalolin tattalin arziƙin da suka addabi ƙasar nan
  • Ɗan majalisar ya bayyana cewa nan ba da jimawa ƙoƙarin da shugaban ƙasan yake yi zai haifar da ɗa mai ido

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ibarapa ta Gabas/Ido daga jihar Oyo, Aderemi Oseni, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa ya kamata ƴan Najeriya su ba Shugaba Tinubu ƙarin lokaci domin shawo kan ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya yabi ministan Tinubu, ya fadi nasarorin da ya samu

An bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da Tinubu
Dan majalisa ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Aderemi Oseni ya bayyana cewa duk da wasu manufofin Tinubu na iya zama masu tsauri, amma sun zama dole domin samar da kyakkyawar makoma ga Najeriya, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da shirin N250m na tallafawa masu sana'o'in walda da ayyukan ƙarafa, rahoton jaridar The Punch ta tabbatar.

Ɗan majalisa ya ba ƴan Najeriya shawara

Ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da marawa gwamnatin Tinubu baya duk da matsalolin tattalin arziƙin da ake fuskanta.

Ya nuna ƙwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba ƙoƙarin da Tinubu ke yi na farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan zai haifar da ɗa mai ido.

"Nan ba da jimawa ba ƙoƙarin da Shugaba Tinubu ke yi na gyara ƙasar nan zai haifar da ɗa mai ido."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jam'iyyar NNPP ta ba Tinubu mafita kan halin kunci

"Shugaba Tinubu a matsayinsa na mai son talaka ya damu kan yadda zai inganta rayuwar ƴan Najeriya."

- Aderemi Oseni

NNPP ta ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya nemi taimakon tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar nan.

Sakataren jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dipo Olaoyoku, ya bayyana cewa a fili yake gwamnati mai ci ba ta da isassun dabaru kan yadda za a fitar da Najeriya daga cikin ƙunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng