Manyan Labarai A Yau
Wasu manyan lauyoyi sun tofa albarkacin bakinsu kan matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na sanya dokar ta baci a jihar Rivers mai arzikin mai.
Wasu fusatattun masu zanga-zanga sun nuna bacin ransu kan kisan da 'yan bindiga suka yi wa manoma a jihar Ondo. Sun mamaye gidan gwamnatin jihar.
Kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP sun nuna rashin jin dadinsu kan dakatarwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar Rivers tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar dokoki.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Mista Peter Obi ya buɗe shafin TikTok, ya samu mabiya mutane sama da 6,000 cikin ƴan sa'o'i, ya wallafa bidiyo mai ɗauke da saƙo.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani kan rikicin siyasar da ke aukuwa a jihar Rivers. Ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya kori hadimai biyu daga aiki bayan gani s] da aikata laifukan da suka shafi rashin ladabi, ya buƙaci su bar ofis nan take.
Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen jihar Kaduna, ta musanta zargin da Nasir El-Rufai ya yi na cewa gwamnatin Uba Sani na sata.
Babban jigo a jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya, Buba Galadima, ya yi magana kan hadakar da jam'iyyun adawa ke shirin yi don kwace mulki a hannun APC.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari