Manyan Labarai A Yau
Hukumar kididdiga ta ƙasa watau NBS ta ce an kara samum raguwar farashin kayayyaki a Najeriya a watan Fabrairu bayan wanda aƙa samu a watan Janairu, 2025.
An samu barkewar sabon rikici tsakanin masu bautar gargajiya da matasan Musulmi a jihar Plateau. Mutane da dama sun jikkata yayin da aka kona wuraren bauta.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wasu hare-haren da 'yan ta'addan ISWAP suka kai a jihar Borno. Sojojin sun yi ragargaji 'yan ta'addan.
Wasu masu zanga-zanga sun fito kan tituna domin nuna bacin ransu kan mayar da zaman kotun sauraron kararrakin zaben kananan jihar Benue zuwa birnin Abuja.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta gamsu da kamun ludayin salon mulkin Gwamna Uba Sani. Ta ce za ta ci gaba ɗa yi masa addu'a.
Tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas, Dr. Abdul'azeez Olajide Adeniran wanda ka fi sani da Jandor, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan ya fice daga PDP.
An samu bullar wata bakuwar cuta a jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi (KSUTA). Cutar wacce ba a gano kowace iri ba ce ta yi sanadiyyar rasuwar dalibai.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana abin da ya sa a gaba a wajen mulki jihar. Uba Sani ya ce burinsa hidimtawa mutanen da suka zabe shi.
Wani babban kusa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Olatunbosun Oyintiloye, ya bayyana cewa ya kamata 'yan adawa su fahimci wane irin mutum ne Bola Tinubu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari