Manyan Labarai A Yau
Tsohon abokin takarar Muhammadu Buhari, Fasto Tunde Bakare, ya yi magana kan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya ce sun tattauna batutuwa.
Hukumar tsaro ta NSCDC ta tura dakaru na musamman 28,000 a sassan Najeriya domin tabbatar da an yi shagalin sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Karamin ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle, ya yi rabo ga mambobin jam'iyyar APC a jihar Zamfara. Matawalle ya raba musu kyautar raguna don bukukuwan Sallah.
Gwamnatin jihar Jigawa ta samu nasarar tsaftace bangaren ma'aikatanta. Gwamnatin ta gudanar da bincike inda ta gano dubunnan ma'aikata na bogi da ke karbar albashi.
Wani matashi mai suna, Sabi'u Usman Saurayi, ya bayyana yadda ya tsira daga hannun masu safarar koda. Ya bayyana cewa da kyar ya tsallake rijiya da baya a hannunsu.
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar SDP a zaben 2023, Umar Ardo, ya samo mafita ga 'yan hadaka kan shirin kifar da Tinubu a 2027.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yinmaraba da wasu mambobin tafiyar Kwankwasiyya da suka koma jam'iyyar APC a jihar Kano.
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi martani mai zafi kan kalaman da Nyesom Wike ya yi a kansa. Ya bayyana cewa ba zai yi cacar baki da yara ba.
An shuga jimami bayan barkewar wani rikici a tsakanin manoma da makiyaya a jihar Neja. Rikicin ya jawo an samu asarar rai yayin da aka raunata wasu da dama.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari