Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta dakatar da shugabanta a jihar Edo. Jam'iyyar ta bayyana cewa an dakatar da shi bayan an same shi da wasu laifuffuka.
Jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihar Neja. Farmakin ya jawo an hallaka 'yan bindiga masu yawan gaske.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gamsu da irin goyon da jam'iyyar APC ke samu. Ya bayyana cewa za ta samu kuri'u masu yawa a zaben shekarar 2027.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bukaci 'yan Najeriya su rika sayen kayayyakin da aka kera a gida domin samar da ayyukan yi.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kwararo yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya bayyana cewa babu adawa anjihar wadda ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fusata bayan bukatar da wani dan siyasa ya yi na a yi amfani da siyasar kabilanci don kifar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP, a wani harin kwanton bauna. An kashe 'yan ta'adda masu yawa yayin arangamar.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin neman kujerar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi ikirarin cewa an yi masa magudin zabe a shekarar 2019. Sai dai, an gano cewa ikirarin nasa karya ce.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari