Manyan Labarai A Yau
Majalisar dattawan Najeriya ta tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC). Ta amince da nadin Tinubu.
Sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana kudirinsa na gudanar da sahihin zabe mai inganci a Najeriya.
Jigo a jam'iyyar ADC kuma jarumi a masana'antar finafinan Nollywood, Kenneth Okonkwo, ya bukaci hukumar INEC ta kwace kujerar gwamnan Bayelsa, Duoye Diri.
Peter Obi ya shigar da kara a kotu kan Deji Adeyanju bisa zargin batanci, inda yake neman diyya N1.5bn da rokon afuwa daga lauyan a jaridu da kafafen yada labarai.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan rikicin jam'iyyar adawa ta PDP. Fayose ya bayyana cewa wasu gwamnoni za su yi murabus daga jam'iyyar.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan yin sulhu da 'yan bindiga. Gwamna Radda ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da su ba.
Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bukaci Mai girma Bola Tinubu da ya daina kokarin ganin ya sanya gwamonin PDP sun koma APC.
Fada shugaban kasa ta yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 da ake tunkara. Ta bayyana cewa ba dan siyasar da zai iya kalubalantarsa.
Kano ta yi fice a karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ta samu matsayi na biyu a gaskiya, ta daya a NECO, da ci gaba a tattalin arziki da muhalli a 2025.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari