Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimmin kira ga sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN).
Gwamna Dikko Radda ya nada sababbin kwamishinoni uku da manyan sakatarori takwas a Katsina, inda ya bukaci su yi aiki da gaskiya, amana da tsoron Allah.
Shahararren dan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya bayana cewa ya auren Basira 'Yar Guda. Ya bayyana cewa dama can ba so yake ba.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana dalilin da ya sanya jami'ata suka cafke tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a babbar kotun Abuja.
Farfesa Joash Amupitan ya zama shugaban INEC na kasa a hukumance bayan karbar rantsuwar kama aiki daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu yau Alhamis a Aso Rock.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Obot Akpabio, ya bayyana cewa masu sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, suna yi ne don kishin kasa.
Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, ya musanta satar dukiyar jama'a lokacin da yake kan mulki. Ya bayyana cewa ya tsunduma sana'ar noma da kiwo.
Jagoran kungiyar ta'addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu ya raba gari da tawagar lauyoyinsa yayin da aka dawo zaman kotu kan tuhume-tuhumen da ake masa a Abuja.
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen Ondo ta tabbatar da mutuwar mutum takwas a hadarin wata tirela mai dauke da buhunan siminti ranar Laraba da daddare.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari