Manyan Labarai A Yau
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya nuna cewa da wuya a iya samun shugaban da zai yi nasara idan Mai girma Bola Tinubu ya gaza a mulkin Najeriya.
Mahaifin marigayiya Somtochukwu Maduagwu, ’yar jaridar Arise TV, ya zargi cewa an kashe ’yarsa da gangan, yayin da ’yan sanda suka kama mutum 12 da ake zargi.
Kungiyar dattawan jam'iyyar PDP na Arewacin Najeriya, sun caccaki ministan babban birnin tarayya Abuja. Sun zarge shi da yunkurin ruguza jam'iyyar PDP.
An yi muhawara mai zafi a Majalisar Dattawan Najeriya kan kudirin dokar zubar da ciki a Najeriya, Sanata Akpabio da Natasha sun yi musayar yawu bayan rufe batun.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta kori mataimakin shugabanta da wasu mutane a jihar Kaduna. Jam'iyyar ta zarge su da rashin da'a tare da cin dunduniyarta.
Kamfanin MainPower (MEDL) ya sanar da daukewar wutar lantarki na tsawon kwana 10 a Enugu daga 22 zuwa 31 Oktoba 2025, domin aikin gyara da inganta wuta.
Wasu mutane da ake zargin masu kwacen waya ne sun hallaka wata ma'aikaciyar lafiya a jihar Kaduna. Sun kashe ta ne yayin kokarin kwace wayar hannunta.
Gwamnatin Kamaru ta sanar da cewa za ta gurfanar da matasa akalla 20 da aka kama a kotun soja kan zanga zangar bayan zaben shugaban kasa saboda tayar da tarzoma.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya. Ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari